Ni Na Taimaki Buhari Ya Samu Mulki, Yana Shiga Aso Rock Ya Juya Mani Baya - Ardo

Ni Na Taimaki Buhari Ya Samu Mulki, Yana Shiga Aso Rock Ya Juya Mani Baya - Ardo

  • Dr. Umar Ardo ya yi ikirarin su ne su ka ba Muhammadu Buhari shawarar ya lashe amansa, ya sake neman takara a 2015
  • Bayan zaben 2011, ‘dan takaran na CPC ya yi alkawarin ba zai kuma neman mulki ba, daga baya ya yi watsi da alkawarin na sa
  • Ardo yake cewa ya taka rawar gani wajen hadewar CPC da ACN, hakan ya yi sanadiyyar da Buhari ya zama shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A wata hira da aka yi da Dr. Umar Ardo, ‘dan siyasar ya yi bayanin irin alakarsa da tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Dr. Umar Ardo ya shaidawa Punch cewa yana siyasar akida ne ba ta neman duniya ba, saboda haka ne ya goyi bayan Muhammadu Buhari a 2015.

Kara karanta wannan

Buhari ya ambaci babban rauni 1 da yake da shi wanda ya iya kawo cikas a mulkinsa

Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari a Daura Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Fitaccen ‘dan siyasar wanda ya nemi takarar shugaban kasa da na gwamna ya bayyana cewa shi ne ya kawo shawarar haduwar ACN da CPC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Umar Ardo ya ba Buhari shawarar takara

A cewarsa shi ya ba Buhari shawara ya nemi Bola Tinubu su hada-kai, kuma hakan aka yi a 2012, ya ce akasin abin da mutane su ke tunani.

Ni na kawo maganar takarar Muhammadu Buhari ta hudu, kuma na bada shawarar ya yi bayan ya fito fili ya ce ba zai sake neman mulki ba.

Buhari: Abin da Dr. Ardo ya fada

"Ni na rubuta tsarin da za a bi, na nemo kudi, na dage har aka yi wa APC rajista a ranar 31 ga watan Yuli 2012, sai Tinubu su ka dauka daga nan.
Ni ne na ba Buhari shawarar ya hadu da Tinubu a Maris na 2012, ya yi masa tayin mataimakin shugaban kasa sai a hada CPC da ACN."

Kara karanta wannan

“Da na koma Jamhuriyar Nijar”: Buhari ya magantu kan zaryar da wasu ke yi a gidansa na Daura

- Umar Ardo

Umar Ardo ya ke cewa ba don abin da ya yi ba, da wani lissafin daban ake yi a yau.

Buhari ya ci amana da ya samu mulki?

"Amma ana ayyana sa a matsayin wanda ya lashe zabe, Buhari ya juya mani baya; bai sake gani na ba ko ya nemi ya yi mani sakayya ba.
A siyasa dole ka sakawa wadanda su ka taimaka wajen nasararka. Ba ni aka yi takaran farko ba, amma ni na kawo shawarar takarar karshe."

- Umar Ardo

Zuwa yanzu ba mu ji tsohon shugaban Najeriya ko hadimansa sun tanka Dr. Ardo ba.

Tinubu ya ba 'Yan APC kujera a INEC

Ku na da labari ana zargin cewa daga cikin wadanda Bola Tinubu ya ba kujerar REC a INEC akwai cikakkun ‘Yan jam’iyyar APC da mutanensa.

Saboda zargin an jawo ‘yan siyasa an ba su aikin zabe, wasu su kai karar Bola Tinubu a kotun tarayya a Legas, su na cewa hakan ya saba doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel