Bangaren CPC sun koma rike da Jam’iyyar APC bayan an sauke Shugabanni

Bangaren CPC sun koma rike da Jam’iyyar APC bayan an sauke Shugabanni

- Jam’iyyar APC mai mulki ta ruguza daukacin shugabanninta a fadin Najeriya

- Wannan ya sa aka dauko sabon lalar lissafi a lokacin da ake sharar fagen 2023

- Rahotanni sun fara nuna cewa karfin ikon jam’iyyar APC ya koma sashen CPC

Ruguza shugabannin APC da aka yi a fadin Najeriya ya sa wasu manyan jiga-jigai suna neman karbe ragamar jam’iyyar yayin da ake shirya wa zaben 2023.

Jaridar This Day ta bayyana cewa an samu wasu jagororin da jam’iyyar mai mulki ta ke kokarin koma wa hannunsu a sakamakon tsige tsofaffin shugabanni.

Shugabannin da aka sauke a jihohi da kananan hukumomi da mazabu suna tare da Adams Oshiomhole, wanda shi kuma yake bangaren Bola Ahmed Tinubu.

Tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu, bai cikin majalisar NEC don haka bai da wani tasiri wajen matakin da majalisar kolin jam’iyyar ta ke dauka ba.

KU KARANTA: Dave Umahi zai iya takarar shugaban ƙasa a 2023 - Buhari

Sanin kowa ne cewa jam’iyyar APC gamayyar tsohuwar CPC, ANPP, ACN da ‘yan tawaren PDP ce. Yanzu bangaren CPC tana kokarin mamaye sauran ‘yan tafiyar.

Gwamna Mai Mala Buni da AGF Abubakar Malami, wadanda suke fadar yadda za ayi a jam’iyyar APC a yanzu, duk sun fito ne daga barin tsohuwar jam’iyyar CPC.

Majalisar Oshiomhole da yaransa wadanda su ke biyayya ga barin ACN-Bola Tinubu sun fita daga lissafi da matakin karshe da jam’iyya ta dauka a wajen taron NEC.

Shugaban kasa da bangarensa na CPC, da Gwamnoni sun samu karin karfin iko a jam’iyya, a lokacin da zaren Bola Tinubu yake warware wa tun kafin 2023.

KU KARANTA: Rigimar cikin gidan APC ta ta’azzara a Kwara tsakanin Gwamna da Ministoci

Bangaren CPC sun koma rike da Jam’iyyar APC bayan an sauke Shugabanni
Taron APC Hoto: www.bbc.com/pidgin/tori-53180988
Asali: UGC

Wadanda su ke da-ta-cewa a yanzu su ne za suyi ruwa da tsaki wajen fito da ‘dan takarar APC a zaben 2023, a halin yanzu sashen CPC ce ta fi karfi ba ACN ba.

Kwanaki kun ji Sanata Kashim Shettima ya na cewa an yi gaggawar fara magana a kan wanda zai tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC a zaben 2023.

Tsohon gwamnan na jihar Borno ya ce shugabannin jam'iyyar APC, har da Muhammadu Buhari zasu zauna su tattauna a kan lamarin, kafin a dauki wani mataki.

Sanata Shettima ya bugi kirji, ya fada wa Duniya duniya cewa jam'iyyar APC za tayi nasara a 2023.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel