'Babu Ilimi a Ciki, Ganduje Ya Bayyana Hanya Daya Tak da Su Ka Bi Wurin Nakasa Kwankwaso, Abba Kabir

'Babu Ilimi a Ciki, Ganduje Ya Bayyana Hanya Daya Tak da Su Ka Bi Wurin Nakasa Kwankwaso, Abba Kabir

  • Dakta Abdullahi Ganduje ya bayyana tsarin da su ka bi wurin nakasa Kwankwaso da jami'yyar NNPP a kotu
  • Ganduje ya ce tun farko sun tanadi shaidu inda ya ce Kwankwaso ya yi kuskure wurin siyan fom na takara a latti
  • Wannan na zuwa ne bayan kotun daukaka kara ta kwace kujerar Gwamna Abba Kabir na jihar Kano a jiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Shugaban jami'yyar APC ta kasa, Abdullahi Ganduje ya bayyana hanyar da su ka bi wurin illata Abba Gida Gida.

Ganduje ya bayyana haka ne yayin da ya ke martani kan hukuncin kotun daukaka kara a jiya Juma'a 17 ga watan Nuwamba.

Ganduje ya bayyana tsarin da su ka bi wurin illata Kwankwaso da Abba Kabir
Ganduje ya yi bayani kan hukuncin kotun daukaka kara a Kano. Ganduje Abdullahi, Abba Kabir.
Asali: Facebook

Mene Ganduje ke cewa kan hukuncin Kano?

Kara karanta wannan

Da gaske na hannun daman Atiku ya sauya sheka daga PDP zuwa APC? gaskiya ta bayyana

Dakta Ganduje ya ce sun sani tun a karon farko Rabi'u Kwankwaso ya yi kuskure saboda ya makance a neman takarar shugaban kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce Kwankwaso ya makance a neman takara bai sani ba hukumar INEC ta rufe karbar fom na takara lokacin da ya koma NNPP.

Ya kara da cewa su na sane da hakan amma su ka bari a zuciyarsu sai lokacin da ya dace su yi amfani da ita, cewar Daily Trust.

Wane hanya Ganduje ya bi a kotu?

Ya ce:

"Su na jami'yyar PDP lokacin da rikici ya barke sun fita ba shiri su na neman kawai inda za su tsuguna.
"Rashin sa'a su ka dira a jam'iyyar kayan dadi, saboda gogan nasu nason zama shugaban kasa ta ko wane hali, ya karbi tikitin takara.
"Haka su ka bai wa gwamna tikiti saboda tsabar son mulki ba su sani ba INEC ta rufe karban fom na takara."

Kara karanta wannan

Yan ta'adda fiye da 60 sun mutu yayin da sabon yaki ya barke tsakanin Boko Haram da ISWAP

Ganduje ya ce tun lokacin su ka tanadi komai don irin wannan lokaci, su ka buga takardu su ka mika wa Gawuna da ya ajiye wata rana za su yi amfani.

Ya ce idon su ya kulle da neman mulki ba su yi amfani da ilimi ba, su ku ma su ka mika shaidu ga kotu cewa ba 'yan takara ba ne, Platinum ta tattaro.

Ganduje ya yi martani kan hukuncin kotu a Kano

Kun ji cewa, Dakta Umar Ganduje ya yi martani kan hukuncin kotun zaben gwamna a jihar Kano.

Ganduje ya ce su na jiran NNPP a kotun koli don sake ba su kashi kamar yadda ta faru a kotun daukaka kara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel