Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Jihar Adamawa

Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Jihar Adamawa

  • Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Adamawa ta sanya ranar yanke hukunci kan nasarar gwamna Ahmadu Fintiri
  • 'Yar takarar gwamna a inuwar APC, Aishatu Binani, ce ta shigar da ƙarar tana ƙalubalantar sakamakon da INEC ta bayyana
  • Idan baku manta ba zaben gwamnan Adamawa ya ja hankali sosai bayan REC ya bai wa Sanata Aisha nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Adamawa - Kotun sauraron ƙorafe-korafen zaɓen gwamna ta sanya ranar yanke hukunci kan sahihancin zaben gwamnan jihar Adamawa, Leadership ta ruwaito.

Kotun ta ce a ranar 28 ga watan Oktoba, zata yanke hukunci kan ƙarar da Sanata Aishatu Binani, ta kalubalanci nasarar gwamna Ahmadu Fintiri a zaben da ya gabata.

Gwamna Ahmed Fintiri da Sanata Aishatu Binani.
Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Jihar Adamawa Hoto: Ahmadu Umaru Fintiri, Senator Aishatu Binani
Asali: Facebook

Sanata Binani, ƴar takarar gwamna ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC ta shigar da ƙara, inda ta nuna ba ta gamsu da nasarar Gwamna Fintiri na jam'iyyar PDP ba.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Kwace Kujerar Dan Takarar Gwamnan PDP Na Jihar Imo, Ta Bayyana Dalilanta

Yar takarar APC ta ƙalubalanci matakin hukumar zaɓe INEC na ayyana Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan da aka yi ranar 18 ga watan Maris, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu zarge-zargen da Binani ta yi

Masu shigar da ƙara, Aishatu Binani da APC sun yi zargin cewa an tafka kura-kurai da suka saɓa wa kundin dokokin zaɓe da kuma maguɗi a zaɓen da ya wuce.

Sun kuma roƙi Kotun zaben ta halasta sanarwan kwamishinan zaɓen Adamawa (REC), Hudu Ari, wanda ya ayyana Binani a matsayin wacce ta lashe zaɓe yayin da baturen zaɓe ba ya kusa.

Tun da farko Binani ta bukaci kotun ta yanke hukunci kafin a gurfanar da dakataccen kwamishinan INEC, Hudu Ari, a gaban kuliya bisa zargin sanar da sakamako ba bisa ka'ida ba.

A nasu ɓangaren, PDP da gwamna Fintiri sun shigar da buƙatar Kotu ta yi fatali da ƙarar da jam'iyyar APC da Aisha Binani, suka shigar a gabanta, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Yi Babban Kamu Yayin Da Fitacciyar Jarumar Fina-Finai a Najeriya Ta Koma APC

NNPP Ta Arewa Maso Yamma Ta Goyi Bayan Korar Kwankwaso

A wani rahoton na daban Sanata Rabiu Kwankwaso ya sake shiga matsala a jam'iyyar NNPP yayin da masu ruwa da tsakin Arewa maso Yamma suka juya masa baya.

A wani taro da suka gudanar, jiga-jigan NNPP sun amince da matakin da aka ɗauka na korar Kwankwaso daga jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel