Zaben Kogi: Tsohon Dan Majalisa, Shugabannin Mata Sun Yi Watsi Da Dino Melaye Da PDP, Sun Koma APC

Zaben Kogi: Tsohon Dan Majalisa, Shugabannin Mata Sun Yi Watsi Da Dino Melaye Da PDP, Sun Koma APC

  • Dino Melaye, dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a zaben jihar Kogi mai zuwa ya hadu da gagarumin cikas, yayin da manyan jiga-jigan jam'iyyar suka sauya sheka
  • Ismail Inah, tsohon dan majalisa wanda ya wakilci mazabar Idah a jihar Kogi, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC wata daya kafin zaben
  • Shugabar matan PDP a karamar hukumar Igalamela-Odolu da shugabannin mata a gudumomin yankin suma sun fice zuwa jam'iyya mai mulki

Igalamela-Odolu, jihar Kogi - Dino Melaye, dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a zaben ranar 11 ga watan Nuwamba mai zuwa a jihar Kogi, ya hadu da gagarumin cikas wata daya kafin zaben.

Hakan ya kasance ne bayan manyan jiga-jigan PDP a jihar Kogi sun fara barin jam'iyyar zuwa jam'iyyar APC yan kwanaki kafin zaben.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Tsige Timipre Sylva a Matsayin Dan Takarar Gwamnan APC a Bayelsa

Jiga-jigan PDP sun sauya sheka zuwa APC a jihar Kogi
Zaben Kogi: Tsohon Dan Majalisa, Shugabannin Mata Sun Yi Watsi Da Dino Melaye Da PDP, Sun Koma APC Hoto: Dino Melaye, Yahaya Bello
Asali: Twitter

Hon. Ismail Inah ya yi watsi da Dino Melaye, PDP, ya koma APC

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, Hon. Ismail Inah Hussein, wanda aka fi sani da Soul Lover, dan majalisa da ya wakilci mazabar Idah a jihar Kogi, ya fice daga PDP zuwa APC tare da daruruwan magoya bayansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano tsohon dan majalisar a ranar Juma'a, 6 ga watan Oktoba, sanye da kayan APC da kuma jigon Kogi Abdullahi Bello a yankin Ajaka da ke karamar hukumar Igalamela-Odolu na jihar. Wannan alama ce ta cewar ya had da jam'iyyar APC mai mulki.

Inah, jigo a jam’iyyar PDP a jihar, ya bayyana hukuncinsa na komawa jam’iyyar APC a matsayin burinsa na goyon bayan ci gaban jihar Kogi da Najeriya.

Shugabannin matan PDP a jihar Kogi sun yi watsi da Dino

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Ƙara Yi Wa Jam'iyyun APC da Labour Party Babban Lahani Ana Dab Da Zabe

Haka kuma tsohuwar shugabar mata ta jam’iyyar adawa a karamar hukumar Igalamela tare da shugabannin mata a yankin sun fice daga PDP.

A jawabinsa na maraba da ‘yan jam’iyyar PDP da suka sauya sheka, Baron Okwoli, kwamishinan sufuri na jihar Kogi, ya yabawa Inah da magoya bayansa kan matakin da suka dauka na komawa jam’iyyar APC mai mulki, rahoton The Guardian.

Zaben Kogi: Jigon APC Ya Yi Murabus, Ya Fice Daga Jam'iyyar Zuwa AA

A wani labara makamancin wannan, mun ji cewa wani babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC) daga ƙaramar hukumar Ankpa ta jihar Kogi, Yahaya Ododo, ya sauya sheƙa zuwa Action Alliance (AA).

Jaridar The Cable ta tattaro cewa wannan na zuwa ne yayin da rage wata ɗaya gabanin zaɓen gwamma wanda za a yi ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel