Zaben Kogi: "Ma Tsallake Harin Ƙisa Har Sau Hudu" Sanata Dino Melaye

Zaben Kogi: "Ma Tsallake Harin Ƙisa Har Sau Hudu" Sanata Dino Melaye

  • Sanata Dino Melaye ya yi iƙirarin cewa sau huɗu ana yunƙurin kashe shi yana tsallake wa da ƙyar a jihar Kogi
  • Melaye, ɗan takarar gwamna a inuwar PDP a zaben jihar mai zuwa, ya ce tun da APC ta hau mulki tashin hankali ya zama ruwan dare
  • Ya ce idan PDP ta karɓi mulki a zaɓen 11 ga watan Nuwamba, zata fara haɗa kan mutane wuri ɗaya

Jihar Kogi - Ɗan takarar gwamna a inuwar PDP a zaben jihar Kogi mai zuwa, Sanata Dino Melaye, ya bayyana cewa ya tsallake rijiya da baya a harin kisan da aka kai masa.

Sanata Melaye ya yi wannan furucin ne a wata hira da Arise TV ranar Alhamis, 12 ga watan Oktoba, 2023.

Sanata Dino Melaye, ɗan takarar gwamnan PDP a jihar Kogi.
Zaben Kogi: "Ma Tsallake Harin Ƙisa Har Sau Hudu" Sanata Dino Melaye Hoto: Dino Melaye
Asali: UGC

A cewarsa, tun da aka wayi gari APC ta karbi ragamar mulkin jihar Kogi shekaru bakwai da rabi da suka wuce, rashin zaman lafiya ya zama ruwan dare har mutane sun saba.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Ɗage Gangamin Kamfen Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Bayelsa, Ta Fitar da Sanarwa

A rahoton Vanguard, ɗan takarar PDP, Melaye ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na tsallake rijiya da baya sau huɗu yayin da aka yi yunƙurin kashe ni, akwai ƙararraki 12 a Kotu wanda gwamnatin tarayya ke fafatawa da Dino. An kai mun hari da dama."
"Ba sabon abu bane wannan domin al'adar APC kenan, abin da suke so kar a zauna lafiya. Jihar nan tamu Kogi ta zama abin tsoro kamar mugun jeji wan da ke bukatar sake ginawa nan take."

Zamu ceto Kogi mu sake gina ta - Melaye

Melaye, ɗaya daga cikin na hannun daman Atiku Abubakar, ya ce yana fatan ya bada gudummuwa iyakar iyawarsa domin ceto jihar da yaye wa jama'a halin da suka shiga.

A cewarsa, komai ya lalace a jihar Kogi tunda APC ta ɗare mulki, ta raba kawunan al'umma ta yadda al'amura suka caɓe wanda ba a taba samun irin haka ba a tarihi.

Kara karanta wannan

Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Dira Jihar Arewa, Ya Aike da Kakkausan Saƙo Ga Yan Ta'adda, Ya Ba Su Zaɓi 2

Ɗan takarar ya ƙara da cewa ajandojin PDP sun ƙunshi a fara hada kan jihar, domin taken yakin neman zabensa shi ne, “Kogi daya, makoma daya.

Jam'iyyar APC Ta Dage Yakin Neman Zaben Gwamana a Jihar Bayelsa

A wani rahoton mun kawo muku cewa Jam'iyyar APC ta ɗage gangamin kaddamar da yaƙin neman zaɓen ɗan takararta na gwamna a zaben Baylesa.

Kakakin APC, Felix Morka, ya ce an ɗage kaddamar da kamfen daga.ranar Asabar, za a sanar da sabuwar rana nan gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel