Dalilin da yasa marawa shugaba Buhari baya keda muhimanci - Gwamnan PDP
- Gwamnan jihar Bayelsa ya ce yana da matukar muhimmanci ga 'yan Najeriya su nuna goyon bayansu ga shugaba Buhari
- Gwamnan ya fadi haka ne a sakonsa na sabuwar shekara
- Dickson ya yi fatan alheri ga Najeriya yayin da muke shiga sabuwar shekara a gobe
Gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson, ya bukaci 'yan Najeriya da su nuna goyon bayansu ga gwamnatin shugaba Buhari.
Ya bukaci dukkanin shugabanni da su manta da banbancin jam'iyya domin hadin kan Najeriya.
Dickson ya yi wannan kira ne a sakonsa na sabuwar shekara ga mutanen jihar Bayelsa dama kasa baki daya.
DUBA WANNAN: Sojojin ruwa sun kwato wani jami'insu da diyar sa daga hannun masu garkuwar da mutane
Gwamnan na PDP ya ce "'Yan Najeriya ya kamata su nuna goyon bayansu ga irin kokarin da shugaba Buhari yake yi, musamman a bangaren tattalin arziki. Ya kamata mu dage da yin addu'o'i domin samun daukin ubangiji. Kafin kasarmu ta gyaru sai mun taya shugabanni da addu'o'i yayin da suke kokarin kawo gyara."
Kazalika, Dickson, ya kara da cewa gwamnatinsa tana sane da bukatun mutanen Bayelsa, tare da basu tabbacin cewar ba zai basu kunya ba.
"A madadina da mutanen jihar Bayelsa, ina taya dukkanin 'yan Najeriya murnar shiga sabuwar shekarar 2018."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng