“Ka Halarci Zaman Kotun Zabe Don Nunawa Atiku Goyon Baya”: Melaye Ga Makinde

“Ka Halarci Zaman Kotun Zabe Don Nunawa Atiku Goyon Baya”: Melaye Ga Makinde

  • Dan takarar PDP a zaben gwamnan jihar Kogi mai zuwa, Dino Melaye, ya baiwa Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo sharadi 1 na tabbatar da yunkurinsa na sulhu da Atiku Abubakar
  • A martaninsa ga jawabin Makinde na cewa an fara farfadowa a PDP, Melaye ya bukaci gwamnan da ya halarci zaman kotun zaben shugaban kasa don marawa Atiku da PDP baya
  • Tsohon sanatan ya kuma bukaci yan majalisa na PDP da su aikata hakan suma sannan su tabbatarwa yan Najeriya cewa an fara warkewa a jam'iyyar

Abuja - Dino Melaye, dan takarar gwamna na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben jihar Kogi, ya fada ma Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da ya tabbatar da kalamansa na cewa jam'iyyar ta fara farfado da kanta.

Melaye ya kalubalanci Makinde da ya halarci zaman kotun zaben shugaban kasa na 2023 a Abuja, don nuna goyon baya ga Atiku Abubakar, dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Bayanai Sun Bayyana Yayin da Atiku, Makinde Da Magajin Wike Suka Sa Labule

Jiga-jigan jam'iyyar PDP
“Ka Halarci Zaman Kotun Zabe Don Nunawa Atiku Goyon Baya”: Melaye Ga Makinde Hoto: Atiku Abubakar, Dino Melaye, Seyi Makinde
Asali: Twitter

Melaye ya kalubalanci Makinde da ya nunawa Atiku da PDP baya ta hanyar halartan zaman kotun zabe

Mai niyan zama gwamnan na PDP ya bukaci hakan ne da yake martani ga jawabin Makinde na cewar jam'iyyar ta fara warkewa da kanta gabannin tattaunawar gaba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Makinde ya yi furucin ne a wani taron PDP da ya gudana a jihar Bauchi, inda gwamnonin jam'iyyar suka zabi Bala Muhammed a matsayin shugaban kungiyarsu.

Channels TV ce ta wallafa bidiyon a shafinta na Twitter a ranar Asabar, 3 ga watan Yuni.

Atiku, Melaye da sauran shugabannin PDP sun halarci taron, inda makinde ya yi jawabin sannan Melaye ya kalubalanci gwamnan na jihar Oyo.

Melaye ya ba Makinde da yan majalisar PDP aikin tabbatarwa yan Najeriya cewa jam'iyyar na da hadin kai yanzu

Kara karanta wannan

Kujerar Dan Majalisar Tarayyar Nasarawa: Al Makura Ya Bayyana Gaskiyar Dalilin Da Ya Sa Ya Janye Karar Da Ya Shigar Kotun Zabe

A nashi martanin ga Makinde na cewa "an fara warkewa yanzu", Melaye ya ce:

"Hanyar fara wannan warkewa, zan so haka, idan daga yanzu, mako mai zuwa da makonni biyu masu zuwa za mu kasancewa a kotun zaman zabe, don ganin Gwamna Seyi Makinde, ya shigo harabar kotun sannan ya zauna don goyon bayan dan takararmu da nuna wa yan Najeriya cewa jam'iyyarmu ta fara warkewa."

Sanatan ya kuma bukaci zababbun yan majalisa na PDP da su aikata hakan suma sannan su bibiyi shari'o'insu da dama a kotun zaben don jam'iyyar ta samu karin yan majalisa.

Kalli bidiyon a kasa:

Makinde ya ce gwamnonin PDP sun shirya taka rawar gani don ci gaban jam'iyyar

A baya mun kawo cewa, jam'iyyar PDP ta fara gyara hargitsin da ta shiga a siyasar Najeriya yayin da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, da wasu gwamnonin jam'iyyar, ciki harda fusatattun 'ya'yan jam'iyyar suka gana.

Atiku da zababbun jami'an jam'iyyar, ciki harda Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas sun halarci taron da aka shirya ma zababbun jami'an PDP, inda Gwamna Bala Mohammed na jihar Buachi ma ya hallara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel