Zaben Bayelsa: Gwamna Diri Ya Karbi Masu Sauya Sheka Daga APC da LP

Zaben Bayelsa: Gwamna Diri Ya Karbi Masu Sauya Sheka Daga APC da LP

  • Gwamna Douye Diri ya karɓi tulin masu sauya sheƙa daga jam'iyyun APC da Labour Party zuwa PDP a jihar Bayelsa
  • Wannan na zuwa ne yayin da gwamnan ke fafutukar neman tazarce kan mulki zango na biyu a zaben watan Nuwamba, 2023
  • Tawagar yaƙin neman zaben gwamnan na PDP ta ziyarci garuruwa da dama domin neman ƙuri'un jama'a

Jihar Baylesa - Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya karɓi tawagar masu sauya sheƙa daga manyan jam'iyyun APC da Labour Party.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa gwamna Diri na jam'iyyar PDP ya karɓi masu sauya sheƙar ne yayin da ake tunkarar zaben gwamnan Bayelsa nan da wata guda.

Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa.
Zaben Bayelsa: Gwamna Diri Ya Karbi Masu Sauya Sheka Daga APC da LP Hoto: Douye Diri
Asali: Facebook

Gwamnan ya tarbe su ne a yankin Amassoma da Amatolo da ke karamar hukumar Ijaw ta Kudu a lokacin da jirgin yakin neman zaben sa ya sauka a SILGA.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Tarayya Da Wasu Manyan Shugabannin Mata Sun Ƙara Ruguza Jam'iyyar PDP a Arewa

Shugaban sabbin masu sauya shekar, Suoyo Ebi Omonibo, ya ce sun dauki matakin komawa jam’iyyar PDP ne domin su marawa ayyukan alherin da gwamnati mai ci ke yi a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jiga-jigan da suka koma jam'iyyar PDP

Sauran wadanda suka sauya sheka daga APC zuwa PDP sun hada da Biebo Pino Oyinki, Igo Akpobolokemi, Evans Zidi Ambiowei, Igo Eyibigha, Karikarisei Sunday, da Kemepade Warri.

Sai kuma Mista Samson Ogugu, wanda ya watsar da tafiyar jam'iyyar Labour Party, ya koma jam'iyyar PDP mai mulkin jihar Bayelsa.

Haka kuma, jirgin yakin neman zaben gwamna Diri na PDP ya sauka a mazabar Ogbia ta 3 ranar Litinin da ta gabata inda ya ziyarci wasu al’ummomi domin neman goyon bayan sake zabensa a karo na biyu.

Baya ga neman kuri'un mutane, mai girma gwamnan ya kuma kaddamar da wasu ayyukan raya ƙasa a wasu kauyukan mazaɓar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Babban Jigon APC Ya Yi Murabus, Ya Fice Daga Jam'iyyar Zuwa Tsagin Adawa

Tawagar karkashin jagorancin Darakta-Janar na kamfen Diri/Law, Mitema Obordor, ta shiga Oruma, Otuasega, Emeyal kana suka wuce garin Kolo, hedkwatar mazabar.

Dandazon magoya bayan jam'iyyar PDP ne suka yi cincirindon tarban ɗan takarar su, Gwamna Diri, da abokin gaminsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo, Thisday ta tattaro.

'Dan Majalisar Tarayya Da Wasu Manyan Shugabannin Mata Sun Ƙara.Ruguza Jam'iyyar PDP

A wani labarin na daban Tsohon ɗan majalisar wakilan tarayya da wasu shugabannin mata sun ƙara kassara jam'iyyar PDP a jihar Kogi.

Jiga-jigan siyasar tare da dumbin magoya bayansu sun sauya sheka daga PDP zuwa APC yayin da ake dab da zaɓen gwamna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel