Philip Shaibu: Mataimakin Gwamnan Edo Ya Shiga Sabon Ofis Tare da Addu'a

Philip Shaibu: Mataimakin Gwamnan Edo Ya Shiga Sabon Ofis Tare da Addu'a

  • Philip Shaibu ya koma sabon ofishinsa na mataimakin gwamna wanda ke wajen gidan gwamnatin jihar Edo
  • Mataimakin gwamnan, wanda saɓani da gwamna ya jawo canja masa ofis, ya fara da gudanar da taron addu'o'i a Benin
  • Shaibu da maigidansa Gwamna Obaseki sun samu saɓani kan batun wanda zai gaji kujerar gwamna a zaben 2024 mai zuwa

Jihar Edo - Mataimakin gwamnan jihar Edo, Kwamared Philip Shaibu, ya koma aiki a sabon ofishinsa da ke lamba 7, Osadebey Avenue a Benin, babban birnin jihar.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Shaibu ya fara shiga sabon ofishinsa ne bayan gudanar da addu'o'i na musamman.

Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu.
Philip Shaibu: Mataimakin Gwamnan Edo Ya Shiga Sabon Ofis Tare da Addu'a Hoto: Phiiph Shaibu
Asali: UGC

Abokai, ‘yan uwa da mukarrabansa sun bi sahun mataimakin gwamnan wajen taron addu’o’in da ya gudana karkashin jagorancin manyan Malamai daga Cocin Benin Archdiocese.

Ko meyasa ya shirya taron addu'o'i?

Kara karanta wannan

Babu Wata Yarjejeniya Da Emefiele Kan Dawo da ‘Biliyan 50’, Gwamnatin Tinubu

Kwamared Shaibu ya ce tun asali ya saba gudanar taron addu’o’i lokaci zuwa lokaci tun da ya hau mukamin mataimakin gwamnan jihar, Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa ya shirya addu'oin ne da nufin ƙara godewa Allah da kuma miƙa lamurransa da ke tafe a sabon wata tare da sabon ofishin a hannun Allah.

Yadda rigima ta shiga tsakanin jiga-jigan biyu

Ku tuna cewa Shaibu da shugabansa, Gwamna Godwin Obaseki sun fara takun saƙa ne kan batun wanda zai gaje shi a zaben gwamna na 2024 mai gabatowa.

Bayan rikici ya shiga tsakaninsu, Shaibu ya bukaci wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da gwamnan, majalisar dokokin jihar, da kuma babban alkalin jihar daga shirin tsige shi.

Gwamnan, bai ji daɗin abin da Shaibu ya yi ba, ya kore shi daga ofishinsa, inda ya maida shi zuwa wani sabon ofishi a wajen gidan gwamnati.

Kara karanta wannan

Ka ji kunya: Jigon APC ya caccaki gwamnan Arewa kan zargin FG da tattaunawa da 'yan bindiga

Shaibu ya nemi sasanci da Obaseki

Amma a ranar 21 ga watan Satumba, mataimakin gwamnan ya fito bainar jama'a, ya nemi gafarar gwamnan kuma ya roƙi ya yafe masa kura-kuran da ya yi.

Da yake maida martani, Obaseki ya ce "A matsayina na mai imani, wajibi ne na karbi wannan uzurin saboda kamar yadda suka ce ba a raba mutum da kuskure, amma yin afuwa sai na Allah."

Miji, Mata da 'Ya'yansu Biyu Sun Mutu Sakamakon Wutar Lantarki a Jihar Taraba

A wani rahoton kun ji cewa Magidanci da matarsa da 'ya'yansu biyu sun mutu sakamakon kawo wutar lantarki mai ƙarfi a Jalingo, jihar Taraba.

Hukumar 'yan sanda ta bayyana cewa wasu mutane da yawa sun samu raunuka kuma suna kwance a Asibiti yanzu haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel