Kotun Zaben Gwamnan Jihar Sokoto Za Ta Yanke Hukunci a Ranar Asabar

Kotun Zaben Gwamnan Jihar Sokoto Za Ta Yanke Hukunci a Ranar Asabar

  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Sokoto ta shirya yanke hukuncinta kan koke-koken da ke gabanta
  • Kotun ta sanya ranar Asabar, 30 ga watan Satumba matsayin ranar da za ta yanke hukuncin kan ƙarar da jam'iyyar PDP ta shigar
  • Jam'iyyar PDP da ɗan takararta dai sun shigar da ƙarar ne suna ƙalubalantar nasarar da gwamnan ya samu a zaɓen ranar 18 ga watan Maris

Jihar Sokoto - Kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan Sokoto ta sanya ranar 30 ga Satumban 2023, a matsayin ranar da za ta bayyana hukuncin da ta yanke kan ƙarar da ke ƙalubalantar zaɓen gwamna Ahmed Aliyu.

Hakan na zuwa ne ne bayan kotun ta tanadi hukuncinta a watan Agusta kan ƙarar da Sa’idu Umar na jam'iyyar PDP ya shigar a kan gwamna Aliyu da mataimakinsa, Idris Gobir, cewar rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Raba Gardama Kan Sahihancin Zaben Gwamnan APC a Jihar Arewa

Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan shari'ar gwmanan jihar Sokoto
Kotun zaben za ta zartar da hukuncinta a ranar Asabar Hoto: Ahmed Aliyu
Asali: Facebook

Mai shari'a Haruna Mshelia, shugaban kotun, ya tanadi hukuncinsa bayan ɓangarorin biyu sun samu damar gabatar da bayanansu na ƙarshe a gaban kotun.

Ya sanar da cewa za a sanar da ranar yanke hukunci ga ɓangarorin a watan Satumba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Umar na ƙalubalantar nasarar gwamna Aliyu

Ƙarar da Sa'idu Umar ya shigar dai tana ƙalubalantar nasarar gwamna Aliyu wanda ya yi takara a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da mataimakinsa Gobir.

Umar ya yi zargin cewa Aliyu bai cika sharuɗɗan cancanta tsayawa takara ba, ya kuma yi zargin cewa an tafka maguɗi a zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Yaushe kotun za ta yanke hukuncin?

Wata sanarwa daga sakataren kotun ƙararrakin zaɓen, Sunday Martins, ta tabbatar da cewa za a yanke hukunci kan ƙarar mai lamba EPT/SK/GOV/01/2023 ranar Asabar 30 ga watan Satumba da misalin ƙarfe 9:00 na safe.

Kara karanta wannan

APC Ta Samu Nasara, Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamna a Zaben 2023

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa ba za a bar magoya baya ba, su shiga harabar kotun saboda jami'an tsaro za su taƙaita zirga-zirga, rahoton Thisday ya tabbatar.

Kotu Ta Kori Karar Jam'iyyar APGA Kan Gwamna Nwifuru

A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Ebonyi ta yi fatali da ƙarar da jam'iyyar APGA ta shigar kan gwamna Francis Nwifuru na jam'iyyar APC.

Jam'iyyar APGA da ɗan takararta, Bernard Odoh, sun ƙalubalanci nasarar da gwamnan ya samu a zaɓen ranar 18 ga watan Maris 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng