Kotun Zabe Ta Tanadi Hukuncinta Kan Shari'ar Zaben Gwamna Nwifuru Na Jihar Ebonyi

Kotun Zabe Ta Tanadi Hukuncinta Kan Shari'ar Zaben Gwamna Nwifuru Na Jihar Ebonyi

  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Ebonyi ta tanadi hukuncinta kan ƙalubalantar nasarar ɗan takarar jam'iyyar APC, Francis Nwifuru
  • Ƴan takarar PDP da APGA na ƙalubalantar cewa Nwifuru wanda ya lashe zaɓen, ba cikakken ɗan jam'iyyar APC ba ne a lokacin zaɓen
  • A nasa martanin, lauyoyin ɗan takarar jam'iyyar APC sun bayyana cewa Nwifuru ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC kafin zaɓen fidda gwanin gwamna, sannan zaɓen shi bai saɓa wa ƙa'ida ba

FCT, Abuja - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Ebonyi mai zamanta a Abuja, ta tanadi hukuncinta kan ƙarar da ɗan takarar gwamnan jam'iyyar PDP, Ifeanyi Odili da na jam'iyyar APGA, Farfesa Benard Odoh, suka shigar.

Kotun ta tanadi hukuncin na ta ne bayan dukkanin ɓangarorin sun kammala miƙa bayanansu, cewar rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sake Aikewa Da Sabon Gargadi Ga Sojojin Juyin Mulkin Jamhuriyar Nijar

Kotu ta tanadi hukuncinta kan shari'ar gwamnan Ebonyi
Kotun zaben ta shirya yanke hukuncinta kan zaben gwamna Nwifuru Hoto: @FrancisNwifuru
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa ƴan takarar na PDP da APGA na ƙalubalantar bayyana ɗan takarar APC, Francis Nwifuru a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan na ranar 18 ga watan Maris 2023.

Nwifuru ba ɗan APC ba ne, cewar masu ƙara

Masu shigar da ƙarar na son kotun ta soke nasarar Nwifuru kan dalilin cewa shi ba cikakken ɗan jam'iyyar APC ba ne a lokacin zaɓen.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sun yi zargin cewa gwamnan jam'iyyarsa ba ta ɗauki nauyinsa yadda ya dace ba, inda suka ce har a lokacin zaɓen shi ɗan jam'iyyar PDP ne.

Sai dai, lauyan ɗan takarar na APC, Arthur Okafor, ya bayyana cewa wanda yake wakiltar cikakken ɗan jam'iyyar APC ne kuma ya lashe zaɓen ne a bisa ƙa'ida.

Ya bayyana cewa gwamna Nwifuru lokacin da yake shugaban majalisar dokokin jihar, ya fice daga PDP sannan ya koma APC kafin ya nemi takarar gwamna a jam'iyyar ta APC, rahoton Premium Times ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Tinubu vs Atiku, Obi: An Gargadi Kotun Zaben Shugaban Kasa Kan Yin Hukuncin Da Zai Haifar Da Rikici a Kasa

Kotu Ta Shirya Yanke Hukunci Kan Shari'ar Atiku vs Tinubu

A wani labarin kuma, kotun saurararon ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, ta shirya yanke hukunci kan ƙarar da Atiku Abubakar da jam'iyyar PDP suka shigar da jam'iyyar APC da Bola Tinubu.

Atiku Abubakar yana ƙalubalantar bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen da hukumar zaɓe ta INEC ta yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng