Kakakin Majalisar Osun Ya Tsallake Rijiya da Baya, Jami'ai 4 Sun Ji Raunuka a Hatsarin Mota

Kakakin Majalisar Osun Ya Tsallake Rijiya da Baya, Jami'ai 4 Sun Ji Raunuka a Hatsarin Mota

  • Kakakin majalisar dokokin jihar Osun ya tsallake rijiya da baya yayin da haɗarin mota ya rutsa da ayarinsa a Osogbo ranar Lahadi
  • Wata majiya ta bayyana cewa kakakin ya sha babu abinda ya same shi amma wasu jami'an tsaro huɗu sun samu raunuka
  • Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda, Olamide Tiamiyu, ya tabbatar da haka inda ya ce an sallami jami'ai biyu

Jihar Osun - Shugabar majalisar dokokin jihar Osun, Adewale Egbedun, ya tsallake rijiya da baya yayin da ayarin motocinsa suka gamu hatsari mai muni ranar Lahadi.

The Nation ta tattaro cewa ayarin motocin kakakin majalisar ya gamu haɗarin ne yayin da suke shirin barin Osogbo, babban birnin jihar ranar 24 ga watan Satumba, 2023.

Kakakin majalisar dokokin jihar Osun, Adewale Egbedun.
Kakakin Majalisar Osun Ya Tsallake Rijiya da Baya, Jami'ai 4 Sun Ji Raunuka a Hatsarin Mota Hoto: Punch
Asali: UGC

Rahoto ya nuna cewa aƙalla jami'an tsaro 4 na cikin ayarin shugaban majalisar sun samu raunuka daban-daban sakamakon hatsarin da ya auku, kamar yadda Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Mummunar Gobara Ta Tashi a Kotun Koli Da Ke Birnin Tarayya Abuja, Bidiyo Ya Bayyana

Wane abu ne ya haddasa hatsarin?

Wata majiya da ta nemi a sakaya bayananta ta bayyana cewa hatsarin ya auku ne sakamakon matsalar da tayar wata mota ta samu, ta sauka daga kan hannunta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa ya ce:

"Nan take motar ta bugi motar da kakakin majalisar dokokin ke ciki amma ba ta yi babbar ɓarna ba, a halin yanzu shugaban majalisa na cikin ƙoshin lafiya."
"Sai dai jami'an tsaro huɗu sun ji raunuka kuma tuni aka hanzarta kai su wani Asibiti kuɗi da ke yankin Oke-Baale a cikin birnin Osogbo, inda suke samun kulawa."

Halin da jami'an tsaron ke ciki bayam hatsarin

Yayin da manema labarai suka tuntuɓi jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda reshen jihar Osun, Olamide Tiamiyu, ya tabbatar da aukuwar laramin, inda ya ce:

"Ya faru ne lokacin da kakakin majalisa ke kokarin fita daga Osogbo, zuwa yanzu likitoci sun sallami biyu daga cikin jami'an tsaron da suka ji raunuka."

Kara karanta wannan

An tafka asara yayin da gobara ta lamushe fitaccen kamfanin robobi a jihar kasuwanci

Gwamna Lawal Ya Zargi Hukumomin FG da Tattaunawa da Yan Ta'adda a Zamfara

A wani labarin kuma Gwamna Lawal ya faɗi mutanen da yake zargi daga FG sun fara tattaunawar sulhu da 'yan bindiga a jihar Zamfara.

Dauda Lawal na PDP ya koka da matakin wanda ake zargin wasu hukumomin FG sun ɗauka ba tare da sanin gwamnatin jihar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel