Hanyoyi 3 da Za a Iya Bi Wajen Gyara Harkar Zabe a Najeriya – Ministan Jonathan

Hanyoyi 3 da Za a Iya Bi Wajen Gyara Harkar Zabe a Najeriya – Ministan Jonathan

  • Osita Chidoka ya yi magana a game da yadda INEC ta gudanar da zaben bana, abin bai burge shi ba
  • A matsayin jagora a jam’iyyar PDP, ‘dan takararsa watau Atiku Abubakar ya zo bayan Bola Tinubu
  • Akwai gyare-gyare da Chidoka yake ganin za a iya yi wa dokoki kamar yadda ya gani a kasar waje

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Osita Chidoka ya na cikin jiga-jigan PDP a kudu maso gabashin Najeriya, ya soki hukumar INEC game da yadda aka shirya zaben 2023.

A wata hira da aka yi da Osita Chidoka a tashar Channels kwanan nan, ya nuna rashin gamsuwarsa kan yadda hukumar zaben ta ke yin aiki.

Legit.ng ta saurari hirar da aka yi da tsohon ministan harkokin jirgin saman na Najeriya, sai ta tsakuro wasu a cikin shawarwarin da ya bada.

Kara karanta wannan

An kuma: Sanatan APC ya yi nasara kan PDP a gaban kotu, an yi watsi da duk wani zargi

Zaben2023
Muhammadu Buhari ya mikawa Bola Tinubu mulki Hoto: www.reuters.com
Asali: UGC

Shawarwarin zaben da Chidoka ya kawo

1. Kammala shari’a kafin rantsar da shugaban kasa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kafin a kai ga rantsar da shugaban kasa, Osita Chidoka ya kawo shawarar a kammala duka shari’ar korafin zabe har zuwa matakin kotun koli.

Hakan ya na nufin dole INEC ta shirya zabuka da wuri domin a samu damar zuwa kotu, wasu na ganin alkalai za su fi samun ‘yancin yin gaskiya.

2. ‘Yan takara su samu akalla rabin kuri’u

Tsohon shugaban na hukumar FRSC zai so ‘dan takara ya lashe akalla rabin kuri’un da aka kada kafin a rantsar da shi a matsayin shugaba a Najeriya.

Wannan kuwa zai taimaka wajen rage tasirin raba kan kuri’un da jam’iyyu su ke yi. Idan sai an samu 50% a zabe, shugaban kasa zai fi samun karbuwa.

3. Gyara dokokin Hukumar INEC

Kara karanta wannan

Nasarorin da Gwamnati 7 Ta Samu Cikin ‘Yan Kwanakin da Bola Tinubu Ya yi a Indiya

Muddin ana sha’awar gyara zabuka, ‘dan siyasar ya bada shawarar a rage karfin da aka ba hukumar zabe na INEC ta gudanar da abubuwa yadda ta so.

Hon. Chidoka ya na son ganin ka’idojin INEC sun shiga cikin dokokin zabe na kasa ta yadda za a gudanar da zabuka da na’urorin zamani kuma a fayyace.

Nyesom Wike vs Atiku Abubakar a PDP

Nyesom Wike ya na so ya rugurguza Jam’iyyar PDP ne saboda ya yi takara a zaben 2027, rahoto ya zo cewa wannan shi ne tunanin Pedro Obaseki.

A cewar Obaseki, Wike ya ci amanar Rotimi Amaechi, Goodluck Jonathan, Peter Odili, da Atiku Abubakar, yanzu kuma ya koma wajen Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng