Farfesa Osinbajo Ya Taya Shugaba Tinubu Da Kashim Murnar Samun Nasara A Kotu

Farfesa Osinbajo Ya Taya Shugaba Tinubu Da Kashim Murnar Samun Nasara A Kotu

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya yi martani kan hukuncin kotun sauraran kararrakin zaben shugaban kasa
  • Osinbajo ya taya Shugaba Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima kan nasarar da su ka samu a kotun a ranar Laraba
  • Ya ce yanzu lokaci ya yi da ya kamata 'yan Najeriya su bai wa shugaban hadin kai da goyon baya don ciyar da kasar gaba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya taya Shugaba Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima kan hukuncin kotun zabe.

Osinbajo ya ce wannan nasara a kotun sauraran kararrakin zaben shugaban kasa ta nuna tabbacin karfin dimukradiyya a kasar.

Osinbajo ya yi martani kan nasarar Tinubu da Kashim
Farfesa Osinbajo Ya Yi Martani Kan Nasarar Tinubu Da Kashim A Kotu. Hoto: Farfesa Yemi Osinbajo.
Asali: Facebook

Meye Osinbajo ke cewa kan nasarar Tinubu?

Farfesan ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook a yau Asabar 9 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Zabe: Atiku Ya Yi Sabon Zargi a Kan Kotun Zaben Shugaban Kasa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A ranar Laraba 6 ga watan Satumba ne kotun sauraran kararrakin zaben ta yanke hukunci bayan shafe sa'o'i 12 ana zaman kotun, cewar Vanguard.

Hukuncin kotun ya tabbatar da Shugaba Tinubu a matsayin halastaccen shugaban kasar Najeriya.

'Yan takarar jam'iyyun adawa na PDP da Labour, Atiku Abubakar da Peter Obi ba su amince da hukuncin kotun ba.

Sun dauki aniyar daukaka kara zuwa kotun koli don kwato hakkinsu.

Wace shawara Osinbajo ya bayar kan nasarar Tinubu?

Sanarwar ta ce:

"Ina taya Shugaba Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima murnar nasara a kotun zaben shugaban kasa.
"Wannan hukuncin ya nuna nasarar jamiyyar da kuma dimukradiyya da bin doka a kasar.
"Dimukradiyya ta kara samun karfi ganin yadda 'yan takarar su ka bi doka tare da imani da kotunan mu."

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Atiku Zai Yi Jawabi Ga Yan Najeriya Kan Hukuncin Kotun Zaben Shugaban Kasa

Ya kara da cewa Shugaba Tinubu a yanzu na bukatar hadin kan 'yan Najeriya don ciyar da kasa gaba.

A cewarsa:

"A yanzu kasar mu na bukatar dukkan hadin kan mu don shawo kan matsalolin mu da samun gyara kasar."

Buhari ya yi martani kan nasarar Tinubu

A wani labarin, tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tofa albarkacin bakinsa a game da hukuncin kotun sauraron karar zaben 2023.

A wani jawabi da ya fitar ta bakin kakakinsa, Garba Shehu, ya ce galabar Bola Tinubu da Kashim Shettima nasara ce ga daukakin ‘yan kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel