Atiku Zai Yi Jawabi Kan Hukuncin Kotun Zaben Shugaban Kasa

Atiku Zai Yi Jawabi Kan Hukuncin Kotun Zaben Shugaban Kasa

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar zai yi jawabi ga yan Najeriya bayan hukuncin da kotun zaben shugaban kasa ta yanke
  • A ranar Laraba, 6 ga watan Satumba ne kotun ta tabbatar da nasarar Shugaban kasa Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasar Najeriya
  • Atiku Abubakar da takwaransa na jam'iyyar LP, Peter Obi ne suka shiga kotu don kalubalantar nasarar Tinubu a zaben da aka yi a ranar 15 ga watan Fabrairun 2023

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2023, Atiku Abubakar, zai yi jawabi ga yan Najeriya a ranar Alhamis, 7 ga watan Satumba.

Atiku zai yi magana ne a kan sakamakon hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta yanke a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisar Dattawa Ya Magantu Kan Hukuncin da Kotun Zabe Ta Yanke, Ya Fada Wa Atiku da Obi Mafita

Atiku ya yi jawabi ga yan Najeriya
Atiku Ya Yi Jawabi Kan Hukuncin Kotun Zaben Shugaban Kasa Hoto: @royaltyuso
Asali: Twitter

Atiku na hararar kujerar Tinubu har yanzu

Tare da shi akwai manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP wadanda suka hadu a hedkwatar jam'iyyar da ke Wadata Plaza Abuja.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Atiku wanda ya yi takarar kujerar shugaban kasa akalla sau biyar ba tare da ya taba ci ba, bai cire tsammani wajen kwato kujera ta daya a kasar ba.

Dan siyasar wanda yake haifaffen dan jihar Adamawa ya shirya tabbatarwa duniya cewa shine ainahin wanda ya lashe zaben shugaban kasar na 2023 kuma ana tsammanin zai garzaya kotun koli don neman adalci bayan hukuncin da kotun zaben ta yanke a kansa.

Da take zartar da hukuncinta, kotun zaben ta kori duk kararrakin da ake yi sannan ta tabbatar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin zababben shugaban kasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Atiku, Obi vs Tinubu: Muhimman Abubuwa 4 Da Ya Kamata Shugaban Kasa a Najeriya Ya Zama Yana Dasu

Muhimman abubuwa 4 da ake bukata don zama shugaban kasar Najeriya

A wani labarin, mun ji cewa mai shari'a Abba Mohammed, daya daga cikin alkalan da suka yanke hukunci kan karar da Atiku Abubakar da Peter Obi, suka shigar kan shugaban kasa Bola Tinubu, ya lissafo abubuwa hudu da ake bukata don zama shugaban kasar Najeriya.

Alkalin ya jaddada matsayin sashi na 131 na kundin tsarin mulkin Najeriya kan abubuwa hudu da ake bukata na zama shugaban kasar Najeriya yayin da yake karanto daya daga cikin hukunce-hukunce a zaman kotun zaben na ranar Laraba, 6 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel