Hukuncin Kotun Zabe: Atiku Ya Yi Sabon Zargi a Kan Kotun Zaben Shugaban Kasa

Hukuncin Kotun Zabe: Atiku Ya Yi Sabon Zargi a Kan Kotun Zaben Shugaban Kasa

  • Atiku Abubakar ya zargi kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa da jinkiri wajen sakin kwafin hukuncin da ta yanke a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba
  • Wakilan lauyoyin Atiku ne suka yi wannan ikirari, inda suka tabbatar da rashin samun kwafin hukuncin har zuwa ranar Juma’a 8 ga watan Satumba
  • Phrank Shaibu, na kusa da mai karan, ya bayyana lamarin a matsayin wani yunkuri da kotun zaben ke yi na tauye kokarin Atiku da yan Najeriya na samun adalci

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya koka kan rashin samun kwafin hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa kwanaki uku bayan an zartar da shi.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, Atiku ya yi wannan korafin ne ta hannun lauyoyinsa, wadanda suka tabbatar da cewar har yanzu basu samu ainahin kwafin hukuncin kotun zaben ba zuwa har zuwa ranar Juma'a, 8 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Wike: Abokin Fadan Atiku Ya Yi Wa PDP Shakiyanci a Kan Shari'ar Zaben 2023

Atiku Abubakar ya ce har yanzu basu samu kwafin hukuncin kotun zabe ba
Hukuncin Kotun Zabe: Atiku Ya Yi Sabon Zargi a Kan Kotun Zaben Shugaban Kasa Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Atiku da PDP basu da isasshen lokaci domin doka ta ba su tsawon kwanaki 14 kacal ne su daukaka kara a gaban kotun koli.

Phrank Shaibu ya caccaki kotun zabe

Da yake martani ga ci gaban, mai ba Atiku shawara na musamman kan harkokin labarai, Phrank Shaibu, ya zargi kotun zaben da tauye kokarin Atiku da yan Najeriya na neman adalci ta hanyar kin sakin ainahin kwafin hukuncin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“Muna so mu tunatar da PEPC cewa ta yi fatali da shaidar wasu daga cikin shaidun Atiku a yayin shari’ar da aka yi a kotun matakin farko saboda jawabinsu ya fita daga lokaci.
"Kuma yanzu, ga dukkan alamu, wannan kotun na son a soke karar da Atiku da PDP za su daukaka a kotun koli saboda dalili na kurewar lokaci."

Kara karanta wannan

Yaro Dan Shekara 15 Da Aka Yanke Wa Hukuncin Kisa Ya Nemi Gwamnan Arewa Ya Sa Hannu

Ya ci gaba da tambaya:

"Shin PEPC bata fahimci cewa lauyoyin da ke wakiltan Atiku da PDP suna bukatar nazarin hukuncin kamar yadda yake kunshe a cikin CTC, wanda ke wakiltar sahihan bayanan da aka yi a kotu a ranar Laraba, domin shigar da kararta ba?"

Hadimin Atiku ya yi wa Shettima wankin babban bargo

A wani labarin kuma, mun ji cewa mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya sake shan caccaka kan furucin da ya yi cewa zai yi wa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ritaya zuwa gidan gona bayan kotun zaben shugaban kasa ta yanke hukunci.

Da yake jawabi ga manema labarai a karshen zaman kotu a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba, Shettima, ya bayyana Atiku a matsayin dattijon kasa da ake ganin mutuncinsa wanda bai cancanci ritaya a Dubai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel