Sanusi II Ya Yi Magana, Ya Bayyana ‘Barnar’ da Gwamnatin Buhari Tayi a Shekaru 8

Sanusi II Ya Yi Magana, Ya Bayyana ‘Barnar’ da Gwamnatin Buhari Tayi a Shekaru 8

  • Muhammadu Sanusi II ya yi Allah-wadai da yadda gwamnatin da ta wuce ta rike tattalin arziki
  • Masanin ilmin tattalin ya zargi shugabannin da su ka bar mulki da rashin daukar shawarar kwararru
  • Sanusi II yake cewa an jefa kasar nan a yanayin da duk abin da aka samu ya tafi a biyan bashi

Lagos - Khalifa Muhammadu Sanusi II ya yi buda-bakin azumin maganar da ya yi na tsawon lokaci a kan halin da tattalin arzikin Najeriya yake ciki.

Sarkin Kano na 14 a wani bidiyo da yake yawo a Facebook, ya nuna cewa babu kudin da gwamnati za ta iya biyan tallafin man fetur da aka saba da shi.

Khalifan darikar Tijjaniyan ya ce hanyar samun kudi ba su wuce a kara haraji ko a karbi bashi a hannun CBN ba, wanda hakan zai kara karya Naira.

Kara karanta wannan

Ya za a yi? Davido ya ce kudi ne matsalar Najeriya, ya ba da shawarin mafita

Sanusi II
Sarki Muhammadu Sanusi II Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Sanusi ya fadi 'gaskiyar magana'

Hadimin shugaban Najeriya, Abdulaziz Abdulaziz ya wallafa bidiyon a shafinsa, ko da Mai martaban bai kama sunan Muhammadu Buhari karara ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Idan ku na cewa $1 ta na kan N900, gobe za ta zama N1500, kuma a zo ana cewa Naira ta karye!
To ya za ayi? Dole sai an sha wahala fa. Idan ba haka ba, Naira ta cigaba da karyewa. Tun ta na N150 lokacin da na bar gwamna, yau ta na N900."

- Muhammadu Sanusi II

Gwamnati babu sanin tattalin arziki

A cewar Mai martaba Sanusi II, babu abin da ya jawo kudin Najeriya ya lalace a duniya illa buga ta da babban bankin kasa na CBN ya rika yi a araha.

"Aka tafi da kasa babu masu ilmin tattalin arzikin kasa, kuma idan an fada a ki sauraro.

Kara karanta wannan

Da Gaske Ministan Birnin Tarayya Wike Ya Bada Umarnin Rushe Tashar Motar Jabi Da Ke Abuja?

Ya zama shekara takwas ban da fadanci babu abin da ake yi, kuma ya zama wadanda su ke fadanci su ne su ke sayen Dala a N400, su saida N500-N700."
"Yaro bai taba aikin komai ba, ka ji shi ya na da jiragen sama da gidaje a Dubai da Ingila. Babu abin da ya yi in ban da ya saye Dala ya sayar."

- Muhammadu Sanusi II

Tsohon gwamnan babban bankin CBN ya ce sai da ta kai fiye da 100% na kudin shigan gwamnati su na tafiya a biyan tulin bashin da aka karbo.

Sai da gwamnatin tarayya ta karbo aron N30tr daga bankin CBN, Mai martaba ya ce a karshe aka shiga yanayin da ba za a iya cin wani sabon bashi ba.

Sanusi ya bada shawara ga marasa hali

Sanusi II ya nemi afuwar masu kukan cewa bai yi magana ba, ya na mai karawa da rokon masu hali su rika taimakawa wadanda ba su da wadata.

Kara karanta wannan

Za A Iya Binciken Buhari Da Tsofaffin Shugabanni, A Kuma Canzawa Najeriya Sabon Suna

Basaraken ya ce dole mutane su rage buri, su daina facakar da aka saba yi a baya.

Ina ma ayi irin na Nijar a Najeriya

Charles Oputa zai so sojojin Najeriya su yi juyin mulki, mawakin ya na so a hambarar da Bola Tinubu wanda ya tika gwaninsa da kasa a zaben 2023.

Magoya bayan Atiku Abubakar da Peter Obi su na zargin shugaba Tinubu da lashe zabe da magudi, yanzu haka ana kotun sauraron korafin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel