Atiku, Obi vs Tinubu: Muhimman Abubuwa 4 Da Ya Kamata Shugaban Kasa a Najeriya Ya Zama Yana Dasu

Atiku, Obi vs Tinubu: Muhimman Abubuwa 4 Da Ya Kamata Shugaban Kasa a Najeriya Ya Zama Yana Dasu

  • A ranar Laraba, 6 ga watan Satumba ne kotun da ke sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta yanke hukunci kan shari'ar Atiku Abubakar, Peter Obi da Bola Tinubu
  • Alkalin kotun zaben, Mai shari'a Abba Mohammed ya jero wasu abubuwan da ake bukata daga dan Najeriya don zama shugaban kasar
  • Daga cikin abubuwan da ake bukata don zama shugaban kasar shine mutum ya kasance haifaffen dan Najeriya

Mai shari'a Abba Mohammed, daya daga cikin alkalan da suka yanke hukunci kan karar da Atiku Abubakar da Peter Obi, na jam'iyyun PDP da Labour Party (LP) suka shigar kan shugaban kasa Bola Tinubu, ya lissafo abubuwa hudu da ake bukata don zama shugaban kasar Najeriya.

Alkalin ya jaddada matsayin sashi na 131 na kundin tsarin mulkin Najeriya kan abubuwa hudu da ake bukata na zama shugaban kasar Najeriya yayin da yake karanto daya daga cikin hukunce-hukunce a zaman kotun zaben na ranar Laraba, 6 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Jerin Alkalan Kotun Koli 13 Da Za Su Bayyana Sahihin Shugaban Najeriya A Gaba, Bayan Daukaka Kara

Abubuwan da ake bukata daga shugaban kasa
Atiku, Obi vs Tinubu: Muhimman Abubuwa 4 Da Ya Kamata Shugaban Kasa a Najeriya Ya Zama Yana Dasu Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Peter Obi
Asali: Facebook

Abun da ake bukata don zama shugaban kasar Najeriya

A cewar alkalin kotun daukaka karar, duk dan Najeriyan da ya cika wadannan abubuwa hudu yana iya shiga takarar neman kujerar shugaban kasar Najeriya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ga jerin abubuwan bukata a kasa:

  1. Ya kasance haifaffen dan Najeriya.
  2. Ya kai shekaru talatin da biyar da haihuwa.
  3. Ya kasance dan jam'iyyar siyasa kuma wannan jam'iyyar ce ke daukar nauyinsa.
  4. Ya zamana ya yi karatu ko da matakin sakandare ne ko makamancin haka.

Justis Abba Mohammed ya yanke hukunci a shari'ar Obi da shugaban kasa Tinubu. Ya kori dukkan kararrakin da masu karar suka shigar, yana mai cewa Obi da jam'iyyar Labour Party sun gaza gabatar da shaida don tabbatar ikirarinsu a karar.

Kotun Zabe: Alkalai sun caccaki lauyoyin Peter Obi kan rashin hujjoji

A gefe guda, mun ji cewa kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa a jiya Laraba, 6 ga watan Satumba, ta zartar da hukuncinta kan ƙarar da Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa LP da Atiku Abubakar na PDP suka shigar kan Shugaba Tinubu.

Peter Obi da Atiku suna ƙalubalantar zaben shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samu a zaɓen shugaban ƙasa, na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel