Kashim Shettima Ya Ce Rashin Ingantaccen Shugabanci Ne Ya Janyo Matsalar Tsaro a Arewa Maso Yamma

Kashim Shettima Ya Ce Rashin Ingantaccen Shugabanci Ne Ya Janyo Matsalar Tsaro a Arewa Maso Yamma

  • Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana abinda ke janyo matsalar tsaro a Arewa maso Yamma
  • Kashim ya ce rashin samun ingantaccen shugabanci ne ya ta'azzara matsalar da ake fama da ita a yankin
  • Kashim ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da wata kungiya ta gamayyar 'yan kasuwa a gidan gwamnati

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa rashin samun shugabanci ingantacce ne ya janyo matsalolin tsaro da ake fama da su a jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Shettima ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin wata kungiya ta 'yan kasuwa, haƙar ma'adinai, masana'antu da noma mai suna CONSCCIMA a gidan gwamnati kamar yadda Vanguard ta yi rahoto.

Kashim Shettima ya bayyana abinda ya janyo matsalar tsaro a Arewa maso Yamma
Kashim Shettima ya ce rashin ingantaccen shugabanci ne ya janyo matsalar tsaro a Arewa maso Yammacin Najeriya. Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Sake Ware Biliyoyin Kudade Don Sake Gina Arewa, Ya Bayyana Dalili

Shettima ya fadi yadda za a magance matsalolin tsaron

Shettima ya bayyana cewa sake fasali da kuma sake tsare-tsare ya zama wajibi domin ɗora yankin na Arewa maso Yamma a turbar ci gaba na gaggawa, wanda hakan ba zai yiwu ba sai da shugabanci nagari.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jihohin Arewa maso Yamma dai sun ƙunshi Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Jigawa, Zamfara da kuma jihar Sokoto birnin Shehu.

Sai dai jihohin Katsina, Sokoto da kuma jihar Zamfara, suna fama da matsananciyar matsalar tsaro ta masu garkuwa da mutane da kuma 'yan bindiga da ke kashe mutane babu gaira babu dalili.

Shettima ya buƙaci a yi sabbin tsare-tsare

Da yake ci gaba da jawabi, Kashim Shettima ya ce dole ne duk wasu masu ruwa da tsaki da ke Arewacin Najeriya su zauna domin yin tunani kan yadda za a sake fasalin al'amura a yankin.

Kara karanta wannan

‘Abun da Tinubu ya Fada Mani Bayan Nada Ni Ministan Abuja’, Wike Ya Bayyana

Shettima ya ce dukkanin jawaban da shugaban kungiyar CONSCCIMA wato Dalhatu Abubakar ya yi, jawabai ne da suka shafi rayuwa da zaman lafiyar al'umma.

Shettima ya kuma ƙara da cewa ba za a taɓa samun zaman lafiya ba idan babu ci gaba, haka nan kuma rashin ci gaba zai iya haifar da wani sabon rashin zaman lafiyan.

Hukumar 'yan sanda bukaci a ɗauki ƙarin jami'ai

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan bayanin da babban Sufeton rundunar 'yan sandan Najeriya, Olukayode Egbetokun ya yi na cewa rundunar na buƙatar ƙarin aƙalla jami'ai dubu 190 domin kula da 'yan ƙasa.

Ya ce a yanzu haka duk ɗan sanda ɗaya a Najeriya yana kula da mutane 650 ne saɓanin mutane 460 da Majalisar Dinkin Duniya ta ba da shawara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Online view pixel