“Kwankwaso Na Ta Kamun Kafa Don Ya Zama Ministan Abuja a Gwamnatin Tinubu”: Ganduje Ya Yi Zargi a Bidiyo

“Kwankwaso Na Ta Kamun Kafa Don Ya Zama Ministan Abuja a Gwamnatin Tinubu”: Ganduje Ya Yi Zargi a Bidiyo

  • Shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya caccaki dan takarar shugaban kasa na NNPP, Rabiu Kwankwaso kan zargin hana shi minista da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi
  • Ganduje ya yi ba'a ga Kwankwaso kan rashin samun mukamin minista a majalisar Tinubu duk da ganawar da suka yi da shugaban kasar a baya-bayan nan
  • Tsohon gwamnan na jihar Kano ya bayyana cewa Tinubu ya yi wasa da hankalin Kwankwaso, ganin cewa yana matukar son ya zama ministan Abuja

Abuja - Abdullahi Ganduje, shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ya sake yin shagube ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Sanata Rabiu Kwankwaso.

Ganduje ya yi wa Kwankwaso ba'a kan rashin samun shiga majalisar Tinubu
“Kwankwaso Na Ta Kamun Kafa Don Ya Zama Ministan Abuja a Majalisar Tinubu”: Ganduje Ya Yi Zargi a Bidiyo Hoto: @AbbaM_Abiyos
Asali: Twitter

Ganduje ya caccaki Kwankwaso kan rashin samun mukamin minista duk da cewa yana tare da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Asari Dokubo Ya Ziyarci Shugaban APC Abdullahi Ganduje, Hotuna Da Bayanai Sun Fito

A cikin wani bidiyo da ya yadu a ranar Litinin, 28 ga watan Agusta, tsohon gwamna jihar Kano, Ganduje ya yi ikirarin cewa Kwankwaso ya goyi bayan rusa gine-gine a Kano.

Ganduje ya yi jawabi ne ga wasu masu yi masa biyayya da magoya bayan jam'iyyar daga Kano yayin da suka kai ziyarar bangirma sakatariyar jam'iyyar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A bidiyon mai tsawon minti biyu da sakan 28, Ganduje ya bayyana cewa shugaban kasa Tinubu yana da wayon da zai ga mastuwar Kwankwaso na son zama ministan Abuja na gaba, jaridar Punch ta rahoto.

"Ba wai Abuja yake so a ba shi minista ba?, wai zai dawo da masta-plan wallahi idan aka tambaye shi menene masta-plan bai sani ba. Za mu gyara masta-plan din Kano, dama mun yi wa mutanen Kano alkawari za mu yi rushe-rushe, ko bene dubu ka yi sai mun rushe."

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Bayan Tsohon Shugaban PDP Ya Yi Mutu

Kalli bidiyon Ganduje yayin da yake yi wa Kwankwaso ba'a

Bidiyon wanda tuni ya yadu a soshiyal midiya, ya fara haddasa cece-kuce a tsakanin magoya bayan yan takarar biyu.

Abba Vs Gawuna: Jam'iyyar APC ta roki magoya baya su dauki azumi

A wani labarin, mun ji cewa jam'iyyar APC reshen jihar Kano ta umarci ɗaukacin mambobinta su ɗauki Azumi kana su ƙara matsa ƙaimi wajen roƙon Allah ya sa su samu nasara a Ƙotun zaɓe.

Sakataren APC na jihar, Ibrahim Zakari Sarina, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa tuni 'ya'yan jam'iyyar na haƙiƙa suka fara bin wannan umarni na yin azumi da Addu'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel