Asari Dokubo Ya Kai Wa Shugaban APC Abdullahi Ganduje Ziyarar Taya Murna a Abuja

Asari Dokubo Ya Kai Wa Shugaban APC Abdullahi Ganduje Ziyarar Taya Murna a Abuja

  • Fitaccen ɗan rajin kare haƙƙin yankin Neja-Delta, Asari Dokubo, ya kai wa Abdullahi Ganduje ziyara
  • Dokubo ya kai wa tsohon gwamnan jihar Kano wannan ziyara ne a gidansa da ke Abuja a ranar Lahadin da ta gabata
  • Ya je ne domin ya taya Ganduje murnar nasarar zaman shugaban jam'iyyar APC da ya yi a ranar 3 ga watan Agusta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Fitaccen ɗan rajin kare haƙƙin yankin Neja-Delta, Alhaji Mujahid Asari Dokubo, ya kai wa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ziyara.

Dokubo ya ziyarci Ganduje ne a ranar Lahadi, 27 ga watan Agusta a gidansa da ke Abuja kamar yadda aka wallafa a shafin jam'iyyar wato @OfficialAPCNg na X.

Asari Dokubo ya ziyarci Ganduje a gidansa na Abuja
Asari Dokubo ya ziyarci Ganduje domin taya shi murnar zama sabon shugaban jam'iyyar APC. Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Asari Dokubo ya je taya Ganduje murnar zama shugaban APC

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku Ya Fadi Iya Wa'adin Da Ya Ragewa Bola Tinubu a Kan Kujerar Shugabanci, Ya Ba Shi Shawara

An bayyana cewa Asari Dokubo ya ziyarci Ganduje a gidansa da ke Abuja domin taya shi murnar zama sabon shugaban jam'iyyar APC da ya yi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An dai zabi Ganduje a matsayin shugaba da kuma Ajibola Basiru matsayin sakataren jam'iyyar APC na ƙasa makonni uku da suka gabata.

Zaben na Ganduje da Basiru ya biyo bayan saukar tsohon shugaba da sakataren APC, Abdullahi Adamu da kuma Oyiola Omisore bi da bi.

Ganduje ya sha alwashin warware rikicin da ya kunno kai a APC

A baya Legit.ng ta yi rahoto kan rikicin cikin gida na jam'iyyar APC da shugabanta Abdullahi Umar Ganduje ya sha alwashin warwarewa.

Saɓani ya dai kunno kai ne a cikin jam'iyyar mai mulki jim kaɗan bayan bayyanar sunayen sabbin mambobin kwamitin gudanarwa da jam'iyyar ta zaɓa.

Ganduje bayan ganawa da ya yi da gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, ya bayyana cewa zai warware rikicin jam'iyyar cikin ruwan sanyi.

Kara karanta wannan

Yadda Ganduje Ya Dawo Cikin Lissafin Siyasa, Ya Wargaza Kawancen Kwankwaso-Tinubu

'Yan sanda sun mamaye babbar sakatariyar APC ta ƙasa

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan mamayar da jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya suka yi wa babbar sakatariyar jam'iyyar APC mai mulki ta ƙasa.

Hakan dai ya faru ne a daidai lokacin da jam'iyyar ta APC ke shirin sanar da sabbin mambobin kwamitin gudanarwa (NWC) na ƙasa na da ta zaɓa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng