‘Mashaƙo’: Allurar Rigakafi Miliyan 6 Jihar Kano Ke Buƙata, Abba Kabir Yusuf

‘Mashaƙo’: Allurar Rigakafi Miliyan 6 Jihar Kano Ke Buƙata, Abba Kabir Yusuf

  • Gwamna Abba Gida Gida na jihar Kano, ya bayyana adadin allurar rigakafin cutar Mashaƙo da suke buƙata
  • Ya ce aƙalla suna buƙatar allurar rigakafi miliyan shida domin yaƙi da cutar mashaƙo ta ‘Diptheria’ a jihar
  • Ya bayyana hakan ne a yayin da ya karɓi baƙuncin gidauniyar Bill & Melinda Gates Foundation

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana adadin allurar rigakafin da suke buƙata domin magance cutar mashaƙo ta 'diptheria' da ta addabi jihar.

Ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi wakilan gidauniyar Bill & Melinda Gates Foundation a gidan gwamnatin jihar.

Gwamnatin Kano ta bayyana adadin allurar rigakafin da take buƙata
Gwamnatin Kano ta ce allurar rigakafin mashaƙo miliyan shida take buƙata. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jihar Kano na bukatar allura miliyan 6 don magance Mashaƙo

Abba wanda mataimakinsa Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta, ya bayyana cewa jihar Kano na buƙatar aƙalla allurar rigakafi miliyan 6 domin magance cutar mashaƙo da ta addabi jihar.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Abubuwan Sani Dangane Da Minista Mafi Karancin Shekaru a Cikin Ministocin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya jaddada aniyar Gwamnatin jihar na ganin ta ƙara ƙarfafa haɗakar da ke tsakanin gwamnatin jihar Kano da gidauniyar ta Bill & Melinda Gates Foundation kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin Kano a kwanakin baya, ta ƙaddamar da wasu cibiyoyi guda uku a faɗin jihar da za a riƙa kwantar da waɗanda suka kamu da cutar ta Mashaƙo kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa.

Abba Gida Gida ya tarbi masu zanga-zanga a Kano

A baya Legit.ng ta yi rahoto kan zanga-zangar da wasu matasa suka gudanar a cikin unguwanni har zuwa gidan gwamnatin Kano dangane da shari'ar zaɓen jihar.

Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ne ya tarbi masu zanga-zangar da ke adawa da shirya maguɗi da suke tunanin ana so a yi a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen jihar.

Kara karanta wannan

Aljeriya Na Ba Nijar Wutar Lantarki Kyauta Bayan Najeriya Ta Dai Na Ba Su? Gaskiya Ta Bayyana

Masu zanga-zangar dai na ɗauke ne da kwalaye da aka yi rubuce-rubuce daban-daban a kansu da ke nuna adawa da abinda suke zargin ana shirin aikatawa.

An roki Tinubu ya sa baki kan shari'ar Kano

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan roƙon da wata ƙungiya jama'a ta yi wa shugaban ƙasa kan ya sanya baki a ƙoƙarin murɗe hukuncin shari'ar zaɓen Kano da ake shirin yi.

Ƙungiyar ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu da kar ya bari a yi amfani da shi wajen murɗe hukuncin shari'ar zaɓen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel