‘Ya ‘Yan Fitattun Siyasa 12 da ke Fantamawa, Su na Rike da Manyan Mukamai a Gwamnati

‘Ya ‘Yan Fitattun Siyasa 12 da ke Fantamawa, Su na Rike da Manyan Mukamai a Gwamnati

  • ‘Ya ‘yan gawurtattun ‘yan siyasar kasar nan sun yi amfani da sunan iyayensu wajen shiga gwamnati
  • Akwai yaron tsofaffin Gwamnoni, Sanatoci ko Ministoci da su ka yi takara, kuma su ka lashe zabensu
  • Bayan haka akwai yaran manyan da gwamnoni ko shugaban kasa sun jawo su, sun ba su mukamai

Abuja - Ba bakon lamari ba ne a ga yaro ko ‘danuwan ‘dan siyasa ya shiga harkar tafiyar da shugabanci, an saba ganin hakan a fadin Duniya.

A wani dogon rahoto da Daily Trust ta fitar, ta tattaro wasu ‘ya ‘ya da su ka yi amfani da dama da sunan gidajensu, su ka shiga siyasa a kasar nan.

Baya ga takara da samun nasara, wadannan mutane su na kai ko za su samu mukamai masu tsoka a gwamnatocin jihohi ko uwa tarayya.

Kara karanta wannan

100 sun mutu: Yanzu haka 'yan Boko Haram da ISWAP suna can suna ta kwabza yaki a Borno

Yaran siyasa
Yaran na gada a siyasa Hoto: Bello El-Rufai, Hon.Erhiatake Ibori-Suenu
Asali: Facebook

Siyasar iyayen gida a Delta

1. Erhiatake Ibori-Suenu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Erhiatake Ibori-Suenu tayi amfani da sunan mahaifinta, James Ibori, a Yunin 2023 ta zama ‘yar majalisar Ethiope, ita ce shugabar kwamitin NDDC.

2. Marilyn Okowa-Daramola

Kafin mahaifinta ya bar gwamna, Marilyn Okowa-Daramola ta samu takarar ‘yar majalisar Ika ta Arewa maso gabas a majalisar dokoki, ta ci.

3. Orode Uduaghan

Orode Uduaghan wanda mahaifinta ya yi gwamna a baya, ba ta samu tikitin majalisa a PDP ba, amma yanzu ta na cikin kwamsihonin gwamnatin Delta.

4. Ededem Anthony Ani

A lokacin Janar Sani Abacha, Anthony Ani ya rike ministan kudi, yanzu haka yaronsa ya na cikin wadanda za su zama Kwamishonin Kuros Riba.

5. Shuaibu Prince Abubakar Audu

Bola Tinubu ya dauko mutum daga gidan Marigayi Abubakar Audu, zai ba shi minista. Ana daf da zai zama Gwamnan Kogi, Audu ya rasu a 2015.

Kara karanta wannan

Yaran El-Rufai Sun Lallaba Sun Roki Shugaban Kasa ya Ba Shi Kujerar Minista

6. Seun Ashamu

Da Gwamna Seyi Makinde ya tashi zakulo kwamishinoni, ya dauko Seun Ashamu wanda mahaifiyarsa Monsurat Sunmonu ta zama Sanata a Oyo.

7. Ada Chukwu

Kamar yadda mahaifinta ya yi gwamna a Enugu, Ada Sullivan Chimeza ta zama kwamishina a karkashin gwamnatin Peter Mbah kwanan nan.

8. Lyold Ekweremadu

Sanata Ike Ekweremadu wanda yake daure a Ingila ya na da yaro, Lyold wanda ake shirin rantsarwa a matsayin kwamishina a jiharsa ta Enugu.

‘Ya ‘yan manya a majalisar tarayya

9. Bello Nasir El-Rufai

Bello El-Rufai ne yake wakiltar Kaduna ta Arewa a majalisa kuma har ya zama shugaban kwamitin dokokin aikin banki. A Mayu mahaifinsa ya bar mulki.

10. Adegboyega Adefarati

Rahoton ya kawo Hon. Adegboyega Adefarati wanda mahaifinsa ya yi gwamna a jihar Ondo. Masanin tarihin ya na rike da shugabancin kwamiti a majalisa.

11. Olamiju Akala

Adebayo Alao Akala ya samu magaji a jihar Oyo, yadda ya yi gwamna haka yaron da ya haifa, Olamiju Akala ya ke wakiltar mazabarsa a majalisar wakilai.

Kara karanta wannan

Watanni 5 Bayan Zaben 2023, An Bar Jama'a a Duhu Da Atiku Ya Ziyarci Kwankwaso

12. Olumide Osoba

Olumide Osoba ya yi karatu a Legas da Landan, bayan ya yi aiki da NLNG, yanzu ya zama ‘dan majalisa, ya bi sahun mahaifinsa da fara yin gwamna a 1992.

Yaran manya su na takara a 2023

A baya kun ji yadda 'ya ‘yan wasu manyan ‘yan siyasa da tsofaffin masu mulki su ka samu nasara a zaben tsaida gwani domin shiga takarar 2023.

Wasu daga cikin yara, ‘yanuwa da na kusa da ‘yan siyasa irinsu James Ibori, Ayo Fayose, Malam Nasir El-Rufai za su tsaya takara a APC da PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng