‘Yaradua, Ganduje, El-Rufai, Bafarawa: 'Ya 'yan Fitattun 'Yan Siyasa Masu Takara a 2023

‘Yaradua, Ganduje, El-Rufai, Bafarawa: 'Ya 'yan Fitattun 'Yan Siyasa Masu Takara a 2023

  • ‘Ya ‘yan wasu manyan ‘yan siyasa da tsofaffin masu mulki sun samu nasara a zaben tsaida gwani
  • Wasu daga cikin yara, ‘yanuwa da na kusa da ‘yan siyasar za su tsaya takara a APC da PDP a 2023

Mun tattaro sunayen wasu daga cikin wadanda suka lashe zaben gwani:

1. Abdulaziz Yaradua

Kanal Abdulaziz Musa Yaradua mai ritaya ya yi nasarar zama ‘dan takarar APC a zaben kujerar Sanatan Katsina ta tsakiya, kani ne ga tsohon shugaban kasa.

Mahaifinsa Musa Yaradua ya rike Minista a gwamnatin Tafawa Balewa. Baffansa kuma ya zama na biyu a gwamnatin Sojan Janar Olusegun Obasanjo a 1976.

2. Umar Abdullahi Ganduje

Kwanakin baya kun samu labari Injiniya Umar Abdullahi Ganduje ya zama ‘dan takarar APC na majalisar tarayya na mazabar Dawakin Tofa/Rimin Gado/Tofa.

Kara karanta wannan

Hamza Al-Mustapha da Wasu ‘Yan Takara da Ya Kamata a Lura da Su da Kyau a 2023

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abba yana cikin ‘ya ‘yan Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje wanda zai sauka a 2023.

3. Bello El-Rufai

Tun a bayan mun kawo maku rahoto cewa alamu masu karfi sun nuna Bello El-Rufai ne wanda jam'iyyar APC za ta ba takara a yankin Kaduna ta Arewa a 2023.

‘Danuwansa Bashir El-Rufai ya tabbatar da cewa yayan na sa Bello El-Rufai ya lashe zabensa a APC. Bello shi ne babban ‘dan Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

4. Diyar James Ibori

A jihar Delta, kun ji yadda ‘diyar tsohon Gwamna, James Ibori ta yi galaba kan Hadimin Gwamna mai-ci a takarar majalisar wakilan tarayya bayan ta samu kuri’a 46.

Erhiatake Ibori-Suenu, ta doke Hon. Ben Igbakpa wajen samun tikitin jam'iyyar PDP a mazabar Ethiope. Mahaifinta na cikin ‘yan siyasan da ake ji da su a Neja-Delta.

Kara karanta wannan

Kwabar Atiku ta yi ruwa, ya rasa manyan shugabannin PDP a wata jihar Arewa

5. Idris Ajimobi

Ku na da labari cewa Mista Idris Abiola-Ajimobi ne ya zama ‘dan takarar APC na shiyyar Kudu maso yammacin Ibadan II a zaben majalisar dokoki na jihar Oyo.

Idris Abiola-Ajimobi yana cikin ‘ya ‘yan tsohon gwamnan Oyo, Marigayi Sanata Abiola Ajimobi.

‘Yaradua, Ganduje da El-Rufai
Abdulaziz Yaradua, Abba Ganduje da Bello El Rufai
Asali: UGC

6. Yaron Theodore Orji

An ji labari Rt. Hon Chinedum Enyinnaya Orji ya samu tikitin takarar ‘dan majalisar tarayya na mazabar Ikwuano/Umuahia a karkashin jam’iyyar hamayya ta PDP.

A halin yanzu Chinedum Enyinnaya Orji shi ne shugaban majalisar dokoki na jihar Abia. Mahaifin ‘dan majalisar shi ne tsohon gwamnan nan watau Sanata Theodore Orji.

7. Joju Fayose

Zaben fitar da gwanin ‘yan takarar jam’iyyar PDP na jihar Ekiti ya nuna Joju Fayose yana cikin wadanda suka samu tikiti, zai nemi kujera a majalisar tarayya.

Joju Fayose zai wakilci mutanen mazabar tsakiyar Ekiti a majalisar wakikan tarayya idan ya yi galaba a kan sauran ‘yan takaran da za su tsaya a zaben 2023.

Kara karanta wannan

2023: Babu wani Tinubu ko Atiku, ni zan lashe zaben 2023, Kwankwaso ya hango wani haske

8. Marilyn Okowa Daramola

'Diyar Gwamna Ifeanyi Okowa, Barista Marilyn Okowa Daramola ce ‘yar takarar PDP a mazabar Ika ta Arewa maso gabas a zaben majalisar dokokin jihar Delta.

Marilyn Okowa Daramola ta na cikin masu ba Mahaifinta, Sanata Ifeanyi Okowa shawara a gwamnatin Delta. A shekara mai zuwa mahaifinta zai bar ofis.

9. Danuwan Umahi

Austin Umahi shi ne ‘dan takarar APC na zaben majalisar dattawa a zabar Kudancin jihar Ebonyi. Kanin gwamnan mai-ci ya doke Ann Agom-Eze a zaben gwani.

10. Olumide Osoba

Hon. Olumide Osoba ya sake zama ‘dan takaran majalisa na shiyyar Abeokuta North /Odeda/Obafemi-Owode. Mahaifin ‘dan majalisar ya yi gwamna a Ogun.

11. Mustafa Sule Lamido

A jihar Jigawa, an ji yadda Mustafa Sule Lamido ya zama ‘dan takarar gwamna a PDP. Matashin zai nemi kujerar da mahaifinsa ya sauka daga kai a Mayun 2015.

12. Mohammed Abacha

A makon da ya gabata ne rahotanni suka zo cewa ‘Dan tsohon shugaban kasar Najeriya, Mohammed Abacha, ya yi nasara a zaben fitar da gwani a Kano.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na Kasa, Sanata Adamu, Ya Bayyana Magajin Buhari

Mohammed Abacha shi ne ‘dan takarar da jam’iyyar PDP ta tsaida a zaben gwamnan jihar Kano. A bangare guda, ‘yan tawaren PDP sun zabi Sadiq Aminu Wali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel