Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Raddi Ga Masu Zargi An Zalunci Arewa Wajen Nada Ministoci

Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Raddi Ga Masu Zargi An Zalunci Arewa Wajen Nada Ministoci

  • Fadar shugaban kasa ba ta yarda da zargin da ake yi wa gwamnati na rashin adalci a madin Ministoci ba
  • Mai taimakawa shugaban Najeriya wajen yada labarai ya ce yankin ya samu gyara matsalolinsa
  • Abdulaziz Abdulaziz ya ce mutanen Arewa ba su da matsala fiye da ilmi, aikin gona da harkar tsaro

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Tun da aka fitar da mukaman da aka rabawa sababbin ministocin Najeriya, wasu su ke ta magangamu na yabo ko kuwa akasin hakan.

Abdulaziz Abdulaziz wanda shi ne mai taimakawa Bola Ahmed Tinubu a kafofin jaridu, ya maida martani ga wasu masu sukar rabon da aka yi.

Malam Abdulaziz Abdulaziz da yake magana a shafinsa na Facebook a safiyar Alhamis, ya wanke mai gidansa daga zargin fifita yankinsa.

Ministocin Fadar Shugaban Kasa
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya nada Ministoci hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Hadimin mai girma shugaban Najeriya ya ce Arewa ba ta da matsalolin da su ka wuce ilmin zamani, tsaro da noma, kuma su na hannunsu.

Kara karanta wannan

Wahalar da Ake Sha Tamkar Nakuda ce, Bola Tinubu Ya Ce Za a Haifi Jariri

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ministocin da su ka fito daga wannan yanki za su samu damar inganta wadannan bangarori.

Kwararren ‘dan jaridar ya na ganin ‘yan siyasa kuma magoya bayan Atiku Abubakar ne su ke amfani da sunan kishin Arewa saboda manufarsu.

Jawabin Hadimin shugaban kasa

“Me ye matsalar Arewa? Tsaro, ilimi da bunƙasa aikin noma.
To duk waɗannan manyan ma’aikatu guda uku an danƙa su a hannun mutanen Arewa amma wani mai son rai zai ce ba a kyautawa Arewa ba.
Watau dai har yau ƴan Atiku Is Coming ba za su daina ci da ceto da sunan Arewa ba. Allah ya kyauta!”

- Abdulaziz Abdulaziz

Tinubu ya rike ma'aikatar fetur

Ku na da labari Bola Tinubu wanda ya fito daga Kudu maso yamma, ya dauki aro wajen Muhammadu Buhari, bai bada babbar Ministan fetur ba.

Akwai masu ra’ayin cewa duk da tulin kuri’un da jihohin Arewa su ka bada a zaben 2023, ba a su rikon ma’aikatun da su ka kira masu tsoka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng