Tsofaffin Ministocin Buhari Da Jonathan 4 Da Suka Samu Mukami a Gwamnatin Tinubu

Tsofaffin Ministocin Buhari Da Jonathan 4 Da Suka Samu Mukami a Gwamnatin Tinubu

FCT, Abuja - A ranar Laraba, 16 ga watan Agusta ne Shugaba Bola Tinubu ya sanar da muƙaman da ya bai wa ministocinsa 45 da aka tabbatar.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

A kwanakin baya ne Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da sunayen mutane 45 cikin 48 da Tinubu zai naɗa matsayin ministoci.

Hudu daga cikin mutane 45 da aka tantance sun taɓa riƙe muƙaman ministoci a lokacin gwamnatocin Buhari da Goodluck Jonathan.

Ministocin Tinubu 4 da suka taɓa riƙe muƙaman ministoci a baya
Wike, Keyamo, da Pate sun riƙe muƙaman ministoci a gwamnanatocin baya. Hoto: Nyesom Wike, Festus Keyamo, @muhammadpate
Asali: UGC

Tsofaffin Ministocin Buhari da Jonathan 4 da suka shiga gwamnatin Tinubu

1. Ali Pate

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakta Ali Pate daga jihar Bauchi, shi ne aka bai wa ministan lafiya da walwalar al'umma na ƙasa.

Ya yi aiki a matsayin ministan lafiya a lokacin Goodluck Jonathan daga shekarar 2011 zuwa 2013.

Kara karanta wannan

Masanin Tattalin Arziƙi Ya Fadi Abinda Zai Faru Idan Ministocin Tinubu Suka Fara Aiki

2. Nyesom Wike

Nyesom Wike shi ne ministan Birnin Tarayya Abuja wanda Tinubu ya zaɓo daga jihar Ribas.

A watan Yulin shekarar 2011 ne Goodluck Jonathan ya naɗa Wike a matsayin ƙaramin ministan ilimi.

A watan Satumbar shekarar 2013 ne kuma tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya ɗaga darajar Wike zuwa babban ministan ilimi na Gwamnatin Tarayya kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

3. Heineken Lokpobiri

Lokpobiri, wanda ya fito daga jihar Bayelsa, ya riƙe muƙamin ƙaramin ministan noma da raya tattalin arziƙin yankunan karkara a lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari da ta shuɗe.

Shi ne kuma wanda ya lashe zaɓen kujerar sanata mai wakiltar Bayelsa ta Yamma a shekarar 2007 a ƙarƙashin jam'iyyar PDP.

A yanzu haka Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Lokpobiri a matsayin ƙaramin ministan man fetur na Najeriya.

4. Festus Keyamo

Festus Keyamo, wanda ɗan asalin jihar Delta ne, ya riƙe muƙamin minista a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Manjo Janar Muhammadu Buhari mai ritaya.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Babban Malamin Addini Ya Fadawa Tinubu Abinda Zai Faru Idan Bai Yi Maganin Halin Da Ake Ciki Ba

A lokacin gwamnatin da ta shuɗe, Festus Keyamo ne ya riƙe muƙamin ministan ƙwadago da ɗaukar ma'aikata na ƙasa kamar yadda Vanguard ta wallafa.

A yanzu haka Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Keyamo a matsayin ministan harkokin sufurin jiragen sama na Najeriya.

An roki Tinubu ya sauya El-Rufai daga Kaduna ta Kudu

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan roƙon da wasu masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC suka yi dangane da gurbin ministan jihar Kaduna da Tinubu zai naɗa.

Masu ruwa da tsakin sun buƙaci Shugaba Tinubu ya maye gurbin Malam Nasir El-Rufai da wani daga cikin 'yan jam'iyyar APC daga Kaduna ta Kudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng

Online view pixel