Cire Tallafi: Babban Malamin Addini Primate Ayodele Ya Gargadi Tinubu Kan Halin Kuncin Da Ake Ciki

Cire Tallafi: Babban Malamin Addini Primate Ayodele Ya Gargadi Tinubu Kan Halin Kuncin Da Ake Ciki

  • An buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya magance halin da Najeriya take ciki na matsin tattalin arziƙi
  • Primate Ayodele ya ce Tinubu ka iya fuskantar bore daga 'yan Najeriya idan bai magance halin matsi da suke ciki ba
  • Ya shawarci Tinubu da kar ya ɗauki maganar a matsayin barazana maimakon shawara domin kare Najeriya daga faɗawa haɗari

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Shugaban INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya aike da wani saƙo mai muhimmanci ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Fitaccen malamin ya yi gargaɗin cewa za a iya samun bore daga 'yan Najeriya idan abubuwa suka ci gaba da tafiya a haka nan da wata uku kamar yadda The Nigerian Tribune ta wallafa.

Primate Ayodele ya faɗawa Tinubu abinda zai faru cikin wata uku idan bai ɗauki mataki ba
Primate Ayodele ya ce 'yan Najeriya za su yi wa Bola Tinubu bore saboda matsin tattalin arziƙi. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Osho Oluwatosin
Asali: Facebook

Primate Ayodele ya gargaɗi Tinubu kan halin da ake ciki

Kara karanta wannan

Masanin Tattalin Arziƙi Ya Fadi Abinda Zai Faru Idan Ministocin Tinubu Suka Fara Aiki

Primate Ayodele ya yi jawabin ne ta hannun mai taiamaka ma sa a kafafen sada zumunta Osho Oluwatosin, inda ya bai wa Bola Tinubu watanni uku ya gyara tattalin arziƙin ƙasa kamar yadda Daily Independent ta wallafa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayyana cewa 'yan Najeriya ba za su jira ƙungiyar ƙwadago ko wasu kungiyoyi su jagorancesu domin yin zanga-zanga ba, inda ya ce da kansu za su fito su cika tituna.

A kalamansa:

“Akwai buƙatar Shugaba Tinubu ya yi duk mai yiwuwa wajen gyara tattalin arziƙi, yana da kyau ya ƙara ƙaimi wajen yin abinda ya kamata saboda matsin tattalin arziƙi zai iya yamutsa Najeriya, kuma hakan zai shafi talaka da mai kuɗi.”

Tinubu na shirin sayar da kamfanonin gwamnati 20

A baya Legit.ng ta kawo rahoto kan shirin da Gwamnatin Tarayya take yi na sayar da aƙalla kamfanoni guda 20 da take da hannun jari mai yawa a ciki.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe: Babban Malamin Addini Ya Bayyana Hanya 1 Da Za a Iya Tsige Shugaba Tinubu

Rahotanni sun nuna cewa kamfanin man Najeriya wato NNPCL, na cikin kamfanonin da Gwamnatin Tarayya ke shirin sayar da hannun jarinta da ke cikinsa.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin ke ƙoƙarin nemo hanyoyin da za ta sake samun isassun kuɗaɗen shigar da za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta da su.

Tinubu ya yi ƙarin haske kan yiwuwar dawo da tallafin man fetur

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan tsokacin da fadar shugaban ƙasa ta yi dangane da batun dawo da tallafin man fetur da aka yayata a farkon makon nan.

Fadar shugaban ƙasar ta ce tallafin man fetur ya riga da ya tafi kenan, babu batun sake dawo da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel