“Hantar PDP Ta Kadu Saboda Ganduje Ya Zama Shugaban APC”, Tsohon Dan Majalisar Kano

“Hantar PDP Ta Kadu Saboda Ganduje Ya Zama Shugaban APC”, Tsohon Dan Majalisar Kano

  • Tsohon ɗan Majalisar Dokokin jihar Kano, Yusuf Suleiman, ya yi wani shaguɓe ga 'ya'yan jam'iyyar PDP
  • Ya ce PDP da ma wasu sauran jam'iyyu na adawa sun shiga tashin hankali saboda samun shugabacin APC da Ganduje ya yi
  • Ya ƙara da cewa Ganduje zai kai jam'iyyar ta APC zuwa mataki na gaba

Kano - Tsohon ɗan Majalisar Dokokin jihar Kano, Yusuf Suleiman ya bayyana cewa zama shugaban jam'iyyar APC da Abdullahi Ganduje ya yi, ya kaɗawa 'yan PDP hanta.

Ya ce hakan ya sanyasu cire musu tunanin dawowa kan kujerar mulki a nan kusa.

Suleiman ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da manema labarai ranar Talata a Kano kamar yadda The Punch ta wallafa.

Ganduje ya ɗagawa 'yan PDP hankali
Zaman Ganduje shugaban APC ya ɗagawa PDP hankali - in ji dan majalisar Kano. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Ganduje Ya Yi Wa Kwankwaso Sabon Shagube Kan Batun Dawowarsa APC

'Yan PDP da sauran 'yan adawa ba su ji dadin zaman Ganduje shugaban APC ba

Ya ce 'yan jam'iyyar PDP da na sauran jam'iyyun adawa da ke yi wa APC mummunar fata, ba su so Ganduje ya zama shugaban jam'iyyar APC ba.

Ya bayyana cewa hakan ne ya tabbatar musu da cewa jam'iyyar ta su ta yi zaɓin da ya dace na wanda zai jagoranceta don cimma nasarori a gaba.

Yusuf ya kuma ƙara da cewa, yana da kyau waɗanda ake ɗaukar nauyinsu domin su faɗi kalamai na ɓatanci a kan Ganduje, su sani cewa za su dawwama a cikin baƙin ciki.

Ganduje zai jagoranci APC zuwa nasara a zaɓukan gwamna da ke ƙaratowa

Yusuf ya kuma ce Abdullahi Ganduje zai jagoranci jam'iyyar ta APC zuwa cimma nasara a zaɓukan jihar Kogi, Bayelsa, Imo da kuma na jihar Edo da za a yi nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Hukumar Kwastam Ta Yi Bayani Kan Dalilin Rufe Iyakokin Najeriya Da Nijar

Ya ce jam'iyyar PDP a jihar Kano ba ta da wani tasirin da har jam'iyyar APC za ta tsaya musayar yawu da ita.

Ya ƙara da cewa idan aka yi duba da abinda sakamakon zaɓen 2023 ya nuna, zai fi dacewa jam'iyyar PDP ta riƙa neman jam'iyyu irinsu PRP da jam'iyyar Labour don tattauna batuwan siyasa ba jam'iyyar APC ba.

Ganduje ya yi wa Kwankwaso shaguɓe kan batun dawowa APC

Legit.ng a baya ta yi rahoton kan shaguɓen da tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso.

A ƙoƙarin ganin ya fusata mabiya ɗariƙar ta Kwankwasiyya, Ganduje ya yi wa shugabansu tayin dawowa APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel