Rufe Kan Iyaka: Ba Faɗa Najeriya Take Da Jamhuriyar Nijar Ba, Hukumar Kwastam Ta Yi Bayani

Rufe Kan Iyaka: Ba Faɗa Najeriya Take Da Jamhuriyar Nijar Ba, Hukumar Kwastam Ta Yi Bayani

  • Hukumar kwastam ta ƙasa, ta ce kulle iyakokin Nijar da Najeriya ta yi ba wai yana nufin yaƙi ba ne
  • Ya ce an rufe iyakokin ne na wucin gadi wanda da zarar an samu daidaito, za a sake buɗewa
  • Rufewar ta shafi duk wasu jihohi ko garuruwa da suka haɗa iyaka da wani gari na jamhuriyar Nijar

Sokoto - Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), ta ce rufe iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Nijar ba shelanta yaƙi ne tsakanin kasashen biyu ba kamar yadda ake hasashe.

Kwanturola janar na wucin gadi na hukumar ta NCS, Mista Adewale Adeniyi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi ga al’ummar iyakar Illela da ke jihar Sokoto ranar Juma’a.

Hukumar kwastam ta yi magana kan juyin mulkin Nijar
Hukumar Kwastam ta ce ba faɗa Najeriya ta ke da jamhuriyar Nijar ba. Hoto: Nigeria Customs Service
Asali: Facebook

Kwanturolan ya zo cika umarnin shugaban ECOWAS ne

Adewale ya ce aikinsa a nan shi ne cika umarnin shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu wanda kuma yake a mazaunin shugaban ƙungiyar ECOWAS.

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Nijar: Hukumar Shige Da Fice Ta Fitar Da Muhimmin Gargaɗi Ga 'Yan Najeriya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce sanin kowa ne cewa babban aikin shugaban ECOWAS shi ne ɗabbaƙa harkokin kasuwanci tsakanin ƙasashen Afrika ta Yamma.

Sai dai Adewale ya ce kowa na sane da cewa kasuwanci ba zai yiwu ba a inda babu zaman lafiya kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Adeniyi ya ce ba iyakar Illela kawai abin ya shafa ba

Adeniyi ya kuma bayyana cewa, rufewar ta shafi duk inda Najeriya ta haɗu da Nijar ba wai iya ta Illela kaɗai ba.

Ya ƙara da cewa kulle iyakokin abu ne na wucin gadi zuwa lokacin da za a gama samun matsaya game da rikicin na Nijar.

Ya ƙara jaddada cewa ba yaƙi Najeriya ta ke da Nijar ba, ba a kawo maganar hakan ba ma.

Da yake gabatar da jawabi, Magajin garin na Illela Alhaji Buhari Tukur, ya jinjinawa shugaban na kwastam, inda ya ce mutanen yankin za su ci gaba da bin doka da oda.

Kara karanta wannan

"Yan Najeriya Suna Farin Ciki da Mulkinka" An Faɗa Wa Shugaba Tinubu Halin da Mutane Ke Ciki

The Cable ta ruwaito cewa Nijar ta sanar da buɗe iyakokinta na sama da na ƙasa da ƙasashen Mali, Burkina Faso, Algeria, Libya da Chad a ranar Larabar da ta gabata.

Shehu Sani ya shawarci majalisa dangane da buƙatar Tinubu ta tura sojoji Nijar

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan shawarar da Sanata Shehu Sani ya bai wa Majalisar Dattawan Najeriya kan buƙatar tura dakarun soji jamhuriyar Nijar.

Shehu Sani ya ce yana da kyau majalisar ta tsaya ta duba batun dakyau saboda gudun abinda ka iya zuwa ya dawo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel