Ganduje: 'Zan Fara Aiki Babu Kama Hannun Yaro A Matsayin Shugaban APC'

Ganduje: 'Zan Fara Aiki Babu Kama Hannun Yaro A Matsayin Shugaban APC'

  • Tsohon gwamna jihar Kano kuma sabon shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi alkwarin kawo sauyi a jam’iyyar
  • Ganduje ya bayyana haka ne yayin jawabin godiya bayan an zabe shi sabon shugaban jam’iyyar a babban taron kwamitin masu ruwa da tsaki
  • Ya yi alkawarin kawo wa jam’iyyar nasara a zabukan da ke tunkarar jam’iyyar a jihohin Kogi da Imo da kuma Bayelsa a watan Nuwamba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja – Sabon shugaban jam’iyyar APC mai mulki, Abdullahi Ganduje ya yi alkawarin daidaita al’amura a jam’iyyar don tabbatar da nasara a zabukan jihohi da ke tafe.

A ranar 11 ga watan Nuwamba ne ake sa ran za a yi zabukan jihohin Imo da Kogi da Bayelsa.

Ganduje ya yi alkawarin yin aiki babu kama hannun yaro a matsayin shugaban APC
Tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje Ya Ce Zai Yi Aiki Babu Kama Hannun Yaro. Hoto: TheCable.
Asali: Facebook

Ganduje ya godewa Tinubu da sauran jiga-jigan APC

Kara karanta wannan

Hotunan Ganduje Sun Kai Hedikwata, Tsohon Gwamnan Kano Ya Shirya Karbar APC

Ganduje ya bayyana haka ne yayin jawabin godiya bayan zaban shi sabon shugaban jam’iyyar a dakin taro na Transcorp Hilton da ke Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya godewa Shugaba Tinubu da sauran ‘yan jam’iyya inda ya yi alkawarin cewa dimukradiyya za ta samu gindin zama a lokacinshi, cewar BussinessDay.

Ya kara da cewa zai tabbatar an yi rijistar mambobin jam’iyyar yadda ya dace tare da ba da kulawa wurin gudanarwa da shawo kan matsalolin da ke damun jam'iyyar.

Ganduje ya yi alkawarin yin nasara a zabuka masu zuwa

Tsohon gwamna Ganduje ya yi alkawarin kawo wa jam’iyyar nasara a zabukan da ke tafe a jihohin Kogi da Bayelsa da kuma Imo.

Jihohin uku na daga cikin wadanda ke yin zabensu daban da babban zabe da ake yi a kasar saboda shari’a da aka ta yi a baya.

Kara karanta wannan

Toh fa: Rikici ya kunno, jam'iyyar su Kwankwaso ta rusa shugabancinta a wasu jihohi

Sauran sun hada da jihohin Anambra da Edo da Ekiti da Osun da kuma Ondo, gidan talabijin na Channels ta tattaro.

Jam'iyyar APC Ta Zabi Ganduje A Matsayin Shugabanta Na Kasa

A wani labarin, jam'iyyar APC mai mulki ta zabi tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje shugabanta a matakin kasa.

An zabi Ganduje ne a yau Alhamis 3 ga watan Agusta yayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a Abuja.

Har ila yau, an zabi Ajibola Basiru a matsayin sakataren jam'iyyar na kasa bayan murabus din Iyiola Omisore.

Asali: Legit.ng

Online view pixel