Kotu Zata Yanke Hukunci da Karar Da Peter Obi Ya Kalubalanci Nasarar Tinubu

Kotu Zata Yanke Hukunci da Karar Da Peter Obi Ya Kalubalanci Nasarar Tinubu

  • Bayan dogon lokaci, kotun sauraron korafe-korafen zaben shugaban ƙasa a Najeriya zata yanke hukunci kan ƙarar Peter Obi da LP
  • A zaman ranar Talata, Alkalin kotu mai shari'a Haruna Tsammani ya bayyana cewa nan ba da jima wa ba za a sanar da ranar yanke hukunci
  • Bangaren masu kara da waɗanda ake ƙara sun mika bayanansu na karshe a rubuce, sauran hukunci kaɗai ya rage

FCT Abuja - Kotun sauraron ƙararrakin zaben shugaban kasa a Najeriya ta ƙarƙare sauraron karar da ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party, Peter Obi, ya shigar gabanta.

The Nation ta rahoto cewa Kotun mai zama a Abuja ta ce zata sanar da ranar yanke hukunci kan ƙarar da Obi da LP suka ƙalaubalanci nasarar shugaban ƙasa, Bola Tinubu.

Peter Obi a Kotun sauraron ƙarar zabe.
Kotu Zata Yanke Hukunci da Karar Da Peter Obi Ya Kalubalanci Nasarar Tinubu Hoto: Peter Obi
Asali: UGC

Shugaban kwamitin alƙalai 5, Mai shari'a Haruna Tsammani, ya ce nan ba da jima wa ba zasu faɗa wa kowane bangare ranar yanke hukunci.

Kara karanta wannan

Sunayen Ministoci: Jerin Iyayen Gida Masu Tasowa a Siyasance Da Ka Iya Zama Ministocin Tinubu

Wannan na zuwa ne bayan ɓangaren masu ƙara da waɗanda ake ƙara sun gabatar da rubutaccen bayani na ƙarshe a zaman ranar Talata, 1 ga watan Agusta, 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda zaman Kotun ya gudana yau Talata

Lauyan masu ƙara, Livy Uzoukwu (SAN), ya yi ikirarin cewa waɗanda yake karewa sun tabbatar da tuhumar da suka yi, daga bisani kuma ya roƙi Kotu ta amsa buƙatunsu.

A ɗaya bangaren kuma lauyoyin waɗanda ake ƙara, INEC, Bola Tinubu, Kashim Shettima da jam'iyyar APC sun buƙaci Kotu ta kori ƙarar saboda ko kaɗan bata cancanta ba.

Lauyan INEC, Abubakar Mahmoud (SAN) da lauyan APC, Lateef Fagbemi (SAN) sun yi musun cewa masu kara sun gaza tabbatar da ƙorafinsu da kwararan shaidu.

Bayan haka ne mai shari'a Haruna Tsammani ya faɗa musu cewa za a sanar da kowane ɓangare idan kotu ta zaɓi ranar yanke hukunci kan wannan ƙara, rahoton Tribune ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Bayan Taro a Aso Villa, NLC Ta Yi Magana Kan Janye Zanga-Zanga da Shiga Yajin Aikin da Ta Shirya a Najeriya

Kotu Ta Jingine Yanke Hukunci Kan Karar da Atiku Ya Kalubalanci Nasarar Tinubu

A ɗazu mun kawo muku cewa Kotun zaɓe ta yi magana kan ranar yanke hukunci kan ƙarar da Atiku Abubakar na PDP ya kalubalanci nasarar Bola Ahmed Tinubu.

Alhaji Atiku, mataimakin shugaban ƙasa a tsakanin 1999 zuwa 2007, ya halarci zaman Kotu na yau Talata a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel