Jerin Iyayen Gida Masu Tasowa a Siyasance Da Ka Iya Zama Ministocin Tinubu

Jerin Iyayen Gida Masu Tasowa a Siyasance Da Ka Iya Zama Ministocin Tinubu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunayen ministoci 28 ga majalisar dattawa a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli domin tantacewa.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Majalisar dattawan ta dakatar da hutun da take shirin tafiya inda ta fara tantance ministocin da Shugaba Tinubu ya naɗa.

Iyayen gida a siyasance a cikin ministocin Tinubu
Sunayen ministocin Tinubu da iyayen gida ne a siyasance Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Sai dai, wasu daga cikin ministocin na Shugaba Tinubu, za a iya yi musu kallon iyayen gida ne a siyasance a jihohinsu.

Ga jerinsu a nan ƙasa:

Nasir Ahmad El-Rufai

El-Rufai ya yi mulkin jihar Kaduna har sau biyu daga shekarar 2015 zuwa 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya taɓa yin ministan birnin tarayya Abuja a ƙarƙashin mulkin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo.

Jigon na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya fara kafa daularsa ta siyasa inda ya tabbatar ɗan takararsa, Uba Sani, ya lashe zaɓen gwamnan jihar a zaɓen ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Kara karanta wannan

"Shugaba Tinubu Ba Zai Yi Dana Sanin Nada Ni Minista Ba", Jawabin Wike Yayin Tantance Shi a Majalisa

Nyesom Wike

Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya mulki jihar har sau biyu daga shekarar 2015 zuwa 2023.

Kamar takwaransa El-Rufai, Wike ya taɓa riƙe muƙamin ƙaramin ministan ilmi a ƙarƙashin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan.

Sakamakon babban zaɓen 2023 ya nuna cewa Wike ya fara gina daularsa ta siyasar uban gida a jihar.

Ɗan takarar da yake marawa baya ya gaje shi akan mulkin jihar, sannan da yawa daga cikin kwamishinoninsa an sake naɗa su kan muƙamansu.

Rabiu Kwankwaso

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Nigerian Peoples Party (NNPP) a zaɓen 2023, na daga cikin ƴan siyasar da suka kafa daular siyasar ubangida a jihar Kano.

Kwankwaso ya lallasa jam'iyyar APC mai mulki a jihar a zaɓen gwamnan jihar na ranar 18 ga watan Maris, ta hanyar marawa ɗan takararsa baya.

Haka kuma ƴan takararsa kusan duk su ne suka lashe kujerun ƴan majalisun jiha da na tarayya a jihar.

Kara karanta wannan

Da Dum-Dumi: Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Manyan Alkalai 2 a Najeriya Suka Kwanta Dama

Kamar Wike, Kwankwaso ya shiga tattaunawa da Shugaba Tinubu kafin a rantsar da shi a ƙasar Faransa, sannan akwai yiwuwar zai iya zama minista a gwamnatin APC.

Sanata Ya Nemi Kawowa El-Rufai Cikas a Majalisa

A wani labarin kuma, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ya so ga samu cikas a lokacin da ake tantance shi domin zama minista.

Sanata Sunday Karimi na jihar Kogi ya nemi titsiye tsohon gwamnan da tambayoyi kan matsalar tsaron da ta addabi jihar Kaduna a lokacin mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel