Buhari Bai Yi Gudun Hijira Zuwa Ko Ina Ba, Garba Shehu Ya Yi Cikakken Bayani

Buhari Bai Yi Gudun Hijira Zuwa Ko Ina Ba, Garba Shehu Ya Yi Cikakken Bayani

  • Mai magana da yawun tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya ƙaryata batun hijirar da aka ce ya yi
  • Garba Shehu ya ce Buhari a yanzu haka yana nan a garin Daura kuma cikin iyalansa
  • Ya bayyana labarin da wata jarida ta wallafa a matsayin na ƙarya da aka wallafa ba tare da yin bincike ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Mai magana da yawun tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya musanta raɗe-raɗin da ake na cewa Buhari ya yi gudun hijira zuwa ƙasar waje.

Garba Shehu ya bayyana hakan ne ranar Lahadi, a wani martani da yakewa wata jarida da ta wallafa labarin cewa Buhari ya yi gudun hijira, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Garba Shehu ya karyata labarin gudun hijirar Buhari
Garba Shehu ya ce ba gudun hijira tsohon shugaban kasa Buhari ya yi ba. Hoto: Garba Shehu
Asali: Facebook

Buhari yana Daura - in ji Garba Shehu

Kara karanta wannan

Mmesoma Ejikeme Ta Sharbi Kuka a Yayin Wayar Tarho, Ta Dauki Alkawarin Bayar Da Hakuri, Sabon Bidiyo Ya Bayyana

Shehu ya ce ko kaɗan babu ƙanshin gaskiya a labarin da jaridar ta fitar kan Buharin, inda ya shawarci kafafen yaɗa labarai da su riƙa yin bincike kafin watsa labari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma ƙara da cewa yanzu haka Muhammadu Buhari na Daura tare da iyalansa saɓanin labarin da ake ta yaɗawa.

A labarin da jaridar ta wallafa, ta yi iƙirarin cewa matsalar tsaro ta sa Buhari ya gudu daga garinsa zuwa ƙasar Birtaniya, rahoton da shi ne Garba Shehu ya ƙaryata.

Shehu ya kuma shawarci jaridar da ta ɗauki mataki mai tsauri ko da kuwa na sallamar ma'aikacin nata da ya wallafa labarin ne.

Shehu ya zargi jaridar da rashin gudanar da bincike

Rashin gudanar da cikakken bincike ne ya sa jaridar buga labarin

Ya ce rashin gudanar da cikakken bincike da jaridar ta yi ne ya sa ta wallafa labarin da yake ba na gaskiya ba.

Kara karanta wannan

Wane Hali Yarinya Yar Shekara 14 da Tsohon Gwamna Ya Aura a Najeriya? Bayanai Sun Fito

Daga ƙarshe Garba Shehu ya shawarci jaridar da ta ƙara himma wajen tabbatar da sahihancin labari kafin wallafa shi kamar yadda The Herald ta ruwaito.

A cewarsa:

“Labari guda ɗaya na ƙarya zai iya ɓata sunan jarida da ta ɗauki shekaru masu yawa ta na ginawa.”

Majalisa za ta binciki gwamnatin Muhammadu Buhari

Legit.ng ta kawo wani rahoto a baya da ke bayyana cewa Majalisar Dattawan Najeriya ta sanar da cewa za ta gudanar da bincike a kan gwamnatin da ta gabata.

Majalisar dai za ta gudanar da binciken ne kan wani kamfani Acugas Limited, wanda aka bai wa kwangilar samar da gas a lokacin gwamnatin Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel