Tambuwal, Wammako, Yari Da Wasu Tsoffin Gwamnoni 10 Da Ke Karbar Kudin Fansho Duk Da Suna Majalisar Dattawa

Tambuwal, Wammako, Yari Da Wasu Tsoffin Gwamnoni 10 Da Ke Karbar Kudin Fansho Duk Da Suna Majalisar Dattawa

Birnin Tarayya Abuja - Wani rahoto na nuni da cewa akwai akalla sanatoci 13 da har yanzu ke karbar fansho daga jihohinsu a matsayin tsaffin gwamnoni.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Hakan na kunshe ne a cikin wani rahoto na Arise TV wanda ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Ogun, Gbenga Daniel, ya nemi a dakatar da fanshon shi na gwamna tunda yanzu yana matsayin sanata a Majalisar Dattawa.

An fallasa sunayen tsaffin gwamnonin da ke karbar fansho duk da suna Majalisar Dattawa
An bayyana sunayen tsoffin gwamnoni 13 da ke karbar kudin fansho duk da suna Majalisar Dattawa. Hoto: Aminu Waziri Tambuwal, Dave Nweze Umahi, Otunba Gbenga Daniel
Asali: Facebook

Gbenga ya fallasa yawan kudaden da ake ba tsoffin gwamnoni

Gbenga ya aika da rokon ne cikin wata takarda mai dauke da kwanan wata 14 ga watan Yuni.

A cikin takardar, gwamnan ya bukaci a dakatar da kudin fansho N676,376.95 (Dubu dari shida da saba'in da shida, da dari uku da saba'in da shida, da kwabo casa'in da biyar), na wata-wata da ake ba shi.

Kara karanta wannan

Toh fa: Kamar Ganduje da Abba, gwamnan Arewa ya kafa kwamitin binciken tsohon gwamna

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanatoci 13 da har yanzu ke karbar kudin fanshonsu na gwamna daga jihohinsu

An tattaro jerin sunayen sanatocin da har yanzu ke karbar kudin fansho a matsayin tsaffin gwamnoni, da kuma albashinsu na Majalisar Dattawa kamar yadda Nigerian Tribune ta hada.

1. Godswill Akpabio (Akwa Ibom) 2007 – 2015

Godswill Akpabio ya rike kujerar gwamnan Akwa Ibom na wa'adi biyu a karkashin jam'iyyar PDP.

Haka nan ya kuma rike ministan Neja Delta a lokacin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A yanzu haka, shine shugaban Majalisar Dattawan Najeriya ta 10.

2. Aliyu Wamakko (Sokoto) 2007 – 2015

Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi mataimakin gwamnan Sokoto na tsawon tenuwa biyu, wato daga 1999 zuwa 2006, kafin daga bisani ya zama gwamnan jihar daga 2007 zuwa 2015.

A lokacin da yake gwamnan jihar Sokoto, ya mayar da hankali kan ababen more rayuwa, ilimi da bangaren lafiya a jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Jam'iyyar APC

Yanzu haka shi ne sanatan da ke wakiltar Sokoto ta arewa.

3. Abdulaziz Yari (Zamfara) 2011 – 2019

Abdulaziz Yari Abubakar tsohon gwamnan jihar Zamfara ne da ya mulki jihar daga 2011 zuwa 2019.

A yanzu haka Yari shi ne sanatan da ke wakiltar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawan Najeriya.

Yari ya dauki hankula cikin 'yan kwanakinnan bayan fitowa da ya yi neman shugabancin Majalisar Dattawa.

4. Dave Umahi (Ebonyi) 2015 – 2023

Tsohon gwamnan jihar Ebonyi Dave Umahi, na cikin sanatocin da har yanzu ke amsar fansho daga jiharsu.

Yanzu shi ne sanatan da ke wakiltar Ebonyi ta Kudu a Majalisar Dattawa karkashin jam'iyyar APC.

5. Aminu Tambuwal (Sokoto) 2015 – 2023

Aminu Waziri Tambuwal ya rike mukamin kakakin Majalisar Wakilai kafin rike gwamnan jihar Sokoto na tsawon tenuwa biyu.

A yanzu haka Tambuwal shi ne sanatan da ke wakiltar Sokoto ta Kudu a Majalisar Dattawan Najeriya.

6. Adams Oshiomhole (Edo) 2008 – 2016

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Dakatar Da Gayyatar Da Aka Yi Wa Ganduje Kan Bidiyon Dala

Adams Aliyu Oshiomole, tsohon shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC), kuma tsohon gwamnan jihar Edo daga 2008 zuwa 2016.

A yanzu haka shi ne sanatan da ke wakiltar Edo ta Arewa.

7. Ibrahim Dankwambo (Gombe) 2011 – 2019

Ibrahim Hassan Dankwambo, shi ne sanatan da a yanzu haka ke wakiltar Gombe ta Arewa.

Ya rike matsayin akanta janar na kasa a can baya, kafin zamansa gwamnan jihar Gombe daga 2011 zuwa 2019.

8. Abubakar Bello (Niger) 2015 – 2023

Abubakar Sani Bello ya yi gwamnan jihar Neja daga shekarar 2015 zuwa 2023.

A yanzu haka shi ne sanatan da ke wakiltar Neja ta Arewa a Majalisar Dattawan Najeriya.

9. Orji Kalu (Abia) 1999 – 2007

Orji Uzor Kalu tsohon dan siyasa ne da ya yi gwamnan jihar Abia daga 1999 zuwa 2007 karkashin jam'iyyar PDP.

A yanzu haka shi ne sanatan da ke wakiltar Abia ta Arewa a Majalisar Dattawa.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Ya Rubuta Wasika, Ya Nemi a Daina Biyan Shi Fanshon N670, 000 a Wata

10. Seriake Dickson (Bayelsa) 2012 – 2020

Henry Seriake Dickson tsohon gwamnan jihar Bayelsa ne da ya jagoranci jihar daga 2012 zuwa 2020.

A yanzu haka shi ne sanatan da ke wakiltar Bayelsa ta Yamma a Majalisar Dattawan Najeriya.

11. Ibrahim Gaidam (Yobe) 2009 – 2019

Ibrahim Geidam shi ne tshohon gwamnan jihar Yobe da ya shugabanci jihar daga 2009 zuwa 2019.

Shi ne sanatan da ke wakiltar Yobe ta Gabas a Majalisar Dattawa.

12. Adamu Aliro (Kebbi) 1999 – 2007

Muhammad Adamu Aliero, tsohon gwamnan jihar Kebbi daga 1999 zuwa 2007. Ya rike ministan Babban Birnin Tarayya a lokacin Umaru Musa Yar'adua.

Yanzu haka shi ne sanatan da ke wakiltar Kebbi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa.

13. Danjuma Goje (Gombe) 2003 – 2011

Mohammed Danjuma Goje, shi ne tsohon gwamnan jihar Gombe da ya jagoranci jihar daga 2003 zuwa 2011.

Goje a yanzu haka yana wakiltar Gombe ta Tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya.

Kara karanta wannan

Bidiyon Dala: Gwamnati Ta Janye Ƙarar da ta Haramtawa EFCC Binciken Ganduje

Dan majalisa mai bukata ta musamman ya zama kakakin Majalisar Dokokin jihar Adamawa

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan wani dan majaalisa mai bukata ta musammaan da ya zama kakakin Majalisar Dokokin jihar Adamawa.

Honorabul Bathiya Wesley ya nemi shugabancin kuma ya yi nasara duk da irin yanayin halittarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel