Tsohon Gwamna Ya Rubuta Wasika, Ya Nemi a Daina Biyan Shi Fanshon N670, 000 a Wata

Tsohon Gwamna Ya Rubuta Wasika, Ya Nemi a Daina Biyan Shi Fanshon N670, 000 a Wata

  • Gbenga Daniel ba zai hada fanshon tsohon Gwamna da albashin majalisar dattawa a lokaci daya ba
  • Tsohon Gwamnan ya bukaci Gwamnatin Ogun ta tsaida fansho da alawus dinsa tun da ya zama Sanata
  • Sanata Daniel ya yi Gwamna a jihar tsakanin 2003 da 2011, saboda haka ana biyansa a kowane wata

Abuja - Gbenga Daniel bai bukatar gwamnatin Ogun ta rika biyan shi fansho da duk wani alawus da ya cancanta saboda zamansa tsohon Gwamna.

A dandalin Twitter, Sanata Gbenga Daniel ya sanar da cewa tuni ya rubutawa gwamnatin jihar Ogun wasika cewa a dakatar da biyansa fansho.

Tsohon Gwamnan ya na cikin wadanda su ka lashe zaben majalisar dattawa da aka yi a farkon shekarar nan, yanzu Sanata ne a inuwar jam’iyyar APC.

Tsohon Gwamna
Tsohon Gwamnan Ogun, Gbenga Daniel da Bola Tinubu Hoto: @JustusOGD
Asali: Twitter

Albashi 2 a lokaci 1

Kara karanta wannan

A Maimakon Kujerar Minista, Shehu Sani Ya Fadi Abin da Ya Dace da Tsofaffin Gwamnoni

Ganin zai rika karbar albashi biyu lokaci guda, Sanata Daniel ya rubuta wasika zuwa ga Gwamna Dapo Abiodun cewa a tsaida fansho da alawus dinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Dan siyasar yake cewa hankalinsa ba zai kwanta idan ya lakume wadannan kudi shi kadai ba. A Najeriya, yin hakan bai ci karo da wata doka ba.

Maganar da Daniel ya yi a shafinsa

"Bayan an rantsar da ni a majalisar dattawa, na rubutawa Mai girma Prince Dapo Abiodun MFR, CON wasika a ranar 14 ga watan Yuli 2023
Na sanar da shi matakin da na dauka cewa a dakatar da biya na N676,376.95k a matsayin fansho da albashi na tsawon Gwamna a jihar Ogun.

The Cable ta ce wasikar ta nuna Sanatan bai taba amfana da wasu kudi na dabam bayan fanshon ba.

Daga lokacin da ya bar kujerar Gwamna a 2011, Daniel ya ce bai mori kudin asibiti, zirga-zirga ko na sayen kayan daki daga hannun gwamnati ba.

Kara karanta wannan

Yariman Bakura Ya Sanya Labule Da Shugaba Tinubu, Ya Nemi Wata Alfarma 1 a Madadin 'Yan Bindiga

A wasikar da ya aikawa Gwamna mai-ci, sabon Sanatan ya ce matakin nan da ya dauka na hakura da cin fansho a yanzu ya fi zama kusa da daidai.

Binciken Bidiyon Dala a Kano

A Kano kuwa, rahoton da mu ka samu shi ne an dawo da maganar binciken fai-fen rashawar Daloli a karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Gwamnatin jihar Kano ta na neman ba Hukumar EFCC damar taso Abdullahi Ganduje a gaba. Hakan na faruwa ne bayan an yi canjin Gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel