Bidiyon Dala: Gwamnati Ta Janye Ƙarar da ta Haramtawa EFCC Binciken Ganduje

Bidiyon Dala: Gwamnati Ta Janye Ƙarar da ta Haramtawa EFCC Binciken Ganduje

  • Gwamnatin jihar Kano ta yaye kariyar da Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya samu daga wajen EFCC
  • A baya, an bukaci kotu ta hana hukumar yaki da rashin gaskiya yin bincike a kan bidiyoyin Dala
  • Ana zargin Ganduje da karbar rashawa a lokacin ya na Gwamna, maganar ta dawo sabuwa a yanzu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Gwamnatin jihar Kano ta shigar da takarda a kotun tarayya da ke Kano a kan shari’arta da hukumar EFCC a kan Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

A rahoton da mu ka samu daga This Day, gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta janye karar gwamnati na hana EFCC yin bincike a kan tsohon Gwamnan jihar.

Ana zargin tsohon Gwamna watau Abdullahi Umar Ganduje da karbar cin hanci a sakamakon fitowar wasu faifen bidiyo tun a cikin shekarar 2018.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Aika Sammaci Ga Ganduje Kan Bidiyon Dala

Kano. Ganduje.
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta binciki Abdullahi Ganduje Hoto: Salisu Yahaya Hotoro
Asali: Facebook

Jaridar ta ce Kwamishinan shari’a kuma babban lauyan Gwamnatin Kano, Haruna Dederi ya shigar da wannan takarda a gaban kotun da ke zama a jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haruna Dederi ya shaidawa kotu cewa ba su da niyyar hana yin bincike a kan batun ko kuma a hana hukuma yi wa wasu jami’an gwamnati tambayoyi.

An tabo shugabannin SUBEB

Jami’an da ke da alaka da zargin karbar rashawar Daloli sun hada da tsohon shugaban SUBEB da Darektan kudi na hukumar da kuma Akanta Janar.

Babbar jami’ar gurfanar da kara ta gwamnatin Kano, Amina Yargaya ta mikawa kotu wannan bukata kamar yadda dokar kotun tarayya ta 2019 ta tanada.

A wancan lokaci, The Guardian ta ce ma’aikatar shari’a ta dauki hayar Sanusi Musa SAN da wasu lauyoyi domin a hana a binciki Dr. Abdullahi Ganduje.

Kara karanta wannan

TETFund: Bayan Shekaru 10, Sababbin ‘Yan Majalisa Za Su Binciki Gwamnatin Jonathan

Gwamnati ta aikawa Lauya takarda

Daderi ya aikawa Sanusi Musa takarda cewa ka da su sake shiga kotu a kan wannan shari’a.

"Mu na sanar da ku mu na neman janye umarnin da mu ka bada a baya a shari’a mai lamba FHC/KN/71/2023 tsakanin babban lauyan gwamnatin Kano da EFCC.
Saboda haka ana umartar kai da abokan aikinka da cewa ka da ku sake daukar wani mataki a kan batun nan, ta hanyar bayyana a kotu ko shigar da wani a kan shari’ar."

- Haruna Dederi

Har zuwa daren yau, ba a tsaida lokacin da kotu za ta saurari bukatar janye wannan kara ba.

Shari'ar zaben jihar Ogun

Wani rahoto da ya dauki hankali a makon nan shi ne wanda lauyan Ladi Adebutu, Goddy Uche (SAN) ya gabatar da shaidunsa a cikin ‘Ghana must go’ a Ogun.

Alkalai uku su ke sauraron karar zaben Gwamnan Ogun a karkashin jagorancin Hamidu Kunaza. Uche ya tafi kotu da shaidu 6000 domin a soke nasarar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel