Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Kwamitin Binciken Gwamnatin Tambuwal

Gwamnatin Sokoto Ta Kafa Kwamitin Binciken Gwamnatin Tambuwal

  • Gwamnan jihar Sokoto ya kafa kwamitin da zai bincike gwamnatin tsohon gwamna Aminu Tambuwal
  • Za a fara bincika abubuwan da suka faru a gwamnatin ne game da siyar da filaye da kadarori masu yawa
  • Ba wannan ne karon farko da sabuwar gwamnati ke bayyana zargi da binciken tsohuwa ba a jihohin Najeriya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Sokoto - Gwamnatin jihar Sokoto ta kafa kwamitin bincike da zai binciko abubuwan da suka faru game da duk wani rabon fili da kadarorin gwamnati da aka yi a zamanin gwamna Aminu Tambuwal.

Kwamitin mai mutum 5 zai kasance ne a karkashin jagorancin mai shari’a M.A. Pindiga (rtd) yayin da Barista Nasiru Muhammed Binji zai kasance sakataren kwamitin.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Cif Jacob E. Ochidi, SAN; Alhaji Usman Abubakar da Barista Lema Sambo Wali, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ta Bayyana: Tambuwal, Yari, Wammako Da Wasu Tsaffin Gwamoni 11 Da Ke Karbar Fanso Bayan Zama Sanatoci

Gwamnan Sokoto zai binciki gwamnatin Tambuwal
Gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu | Hoto: Ahmed Aliyu
Asali: Twitter

Dalilin fara wannan bincike da kafa kwamiti

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran gwamna Ahmed Aliyu ta bayyana cewa, kwamitin zai kuma tantance da bin diddigin asusun gwamnati da adadin da aka samu daga siyar da kadarori da kuma gwanjonsu a jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar ta kara da cewa kwamitin zai yi nazari kan yadda aka raba filaye daban-daban a duk fadin jihar da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Ta ce binciken zai kai ga duba dukkan abubuwan da aka yi da filayen da ke alaka da gwamnati da sauran kadarori.

Yaushe kwamitin zai tattara rahotonsa?

An baiwa kwamitin watanni biyu daga ranar zaman farko da aka gabatar, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

A tun farko, sabuwar gwamnatin jihar Sokoto ta sha alwashin yin bincike da kwa-kwaf din wasu manyan abubuwan da suka faru a gwamnatin Aminu Tambuwal, rahoton ICIR.

Kara karanta wannan

Bidiyon Dala: Gwamnati Ta Janye Ƙarar da ta Haramtawa EFCC Binciken Ganduje

Da alamu wannan ne somin-tabi na wannan bincike, kuma ba wannan ne karon farko da sabuwar gwamnati ke binciken tsohuwa ba a Najeriya.

Abba Gida-Gida ya sha alwashin bincikar gwamnatin Ganduje kan bashin N241bn

A wani labarin, gwamna mai jiran gado na jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ga sja alwashin bincikar bashin N241 da ya gada daga gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.

Yusuf ya bayyana cewa takardun miƙa mulki da gwamna Ganduje ya bayar ta hannun sakataren gwamnatin jihar mai barin gado, sun yi kaɗan kuma ba su da yawa, cewar rahoton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Online view pixel