Gwamnatin Kano Ta Ce Ba Ta Kori Ma'aikata 10,800 Ba, Ta Bayyana Dalilan Dakatar Da Albashinsu

Gwamnatin Kano Ta Ce Ba Ta Kori Ma'aikata 10,800 Ba, Ta Bayyana Dalilan Dakatar Da Albashinsu

  • Gwamnatin jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Abba Gida Gida ta bayyana cewa ba korar ma'aikata 10,800 da Ganduje ya ɗauka ta yi ba
  • Ta bayyana cewa ta dakatar da albashinsu ne kawai domin ta gudanar da bincike kan sabbin ma'aikata da aka ɗauka
  • Gwamnatin ta Abba ta yi zargin cewa gwamnatin da ta gabata ta ɗauki ma'aikata gami da ƙarawa wasu girma ba bisa ƙa'ida ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Abba Gida Gida, ta ce har yanzu ba ta kori ma’aikata 10,800 da ta dakatar da albashinsu a watan Yuni ba.

Ma’aikatan 10,800 dai sune waɗanda gwamnatin tsohon gwamna, dakta Abdullahi Ganduje ta ɗauka aiki, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Gwamnatin Kano ta ce ba ta kori ma'aikata 10,800 ba
Gwamnatin Abba Gida Gida ta ce ba ta kori ma'aikata 10,800 ba. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Bayanin hakan ya fito ne a ranar Juma’a a Kano a yayin wani taron manema labarai na haɗin gwiwa da kwamishinan yaɗa labarai, Malam Baba Dantiye, akanta janar Abdukadir Abdulsalam, da shugaban ma'aikata, Usman Bala-Muhammad suka yi.

Kara karanta wannan

Ana Shagalin Babbar Sallah, Gwamna Ya Dakatar da Wasu Ma'aikata da Babban Shugaba Nan Take

An dakatar da albashin ma'aikata 10,800 ne don gudanar da bincike

Shugaban ma'aikatan ya bayyana cewa ba a kori ma’aikata 10,800 ba, amma dai an dakatar da albashinsu har sai an gama tantance matsayinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

“Ina son in bayyana sarai cewa babu wani ma’aikaci da aka kora. An dakatar da albashinsu ne domin tsaftace tsarin saboda wasu zarge-zarge da ake da su.”
"Nan ba da jimawa ba za a kafa kwamitin tantancewa kuma bayan kammala aikin waɗanda aka ɗauka bisa duk ƙa'idojin aikin gwamnati za su samu albashinsu."

A cewarsa, abin da ake bukata shi ne a inganta ma’aikatan gwamnati domin samun abubuwan da ake so, da kuma ajiye komai inda ya dace.

Da yake tsokaci, Dantiye ya ce gwamnati ta yabawa ma’aikata da ‘yan fansho a jihar bisa haƙurin da suka nuna da kuma farin cikin da suka nuna a lokacin da aka biya su albashin watan Yuni ba tare da an cire musu komai ba.

Kara karanta wannan

Kano: Ganduje Ya Koka Kan Dakatar da Albashin Ma'aikata Sama da 10,000, Ya Tona Wani Sirrin Abba Gida Gida

Gwamnati za ta kori waɗanda aka ɗauka ba bisa ƙa'ida ba

A nasa jawabin, akanta janar ɗin ya bayyana cewa kwamitin da Abba Gida Gida ya kafa zai duba hanyoyin da za a bi domin cire waɗanda aka ɗauka ba bisa ƙa’ida ba.

A cewarsa, gwamnatin da ta shuɗe ta ɗauki ma’aikata da kuma ƙarawa wasu girma ne kawai a lokacin da wa'adinta ya zo ƙarshe.

Abba Gida Gida ya ce bai yi nadama kan rushe-rushen da yake yi ba

Legit.ng a baya ta kawo muku wani labari inda gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da Abba Gida Gida ya bayyana cewa bai yi nadama ba kan duka rushe-rushen da gwamnatinsa ke yi.

Ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya kai masa ziyarar barka da sallah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel