CBN: Ya Kamata Tinubu Ya Fadada Binciken Emefiele Har Zuwa Kan Sanusi, Jigon APC

CBN: Ya Kamata Tinubu Ya Fadada Binciken Emefiele Har Zuwa Kan Sanusi, Jigon APC

  • An bukaci shugaban kasa Bola Tinubu ya binciki tsohon sarkin Kano kuma tsohon gwamnan CBN, Muhammad Sanusi Lamido
  • Jigon APC, Kailani Muhammad, ya jadadda cewar ya kamata Sanusi ya amsa wasu tambayoyi dangane da cire shi daga kujerar gwamnan CBN
  • Muhammad ya bukaci shugaban kasa Tinubu ya daina sauraron Sanusi, cewa duk neman suna yake yi

An shawarci Shugaban Kasa Bola Tinubu da ya fadada binciken da ke gudana a ofishin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele har zuwa zamanin Sanusi Lamido.

Kimanin shekaru tara kenan da sanusi ya rike mukamin gwamnan babban bankin Najeriya har zuwa lokacin da aka sauke shi a 2014.

Shugaban kungiyar goyon bayan Tinubu kuma Darakta Janar na kungiyoyin hadaka na APC, Mista Kailani Muhammad ne ya bayar da shawarar, TVC News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zance ya fito: Bayan Ganawar Tinubu Da Dangote Da Matawalle, Batutuwa Sun Fito Waje

Sanusi Lamido da Shugaban kasa Bola Tinubu
CBN: Ya Kamata Tinubu Ya Fadada Binciken Emefiele Har Zuwa Kan Sanusi, Jigon APC Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Mistan Kailani ya lissafa matsalolin da suka yin sanadiyar tsige Sanusi da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi a 2014, yana mai cewa bai kamata Tinubu ya yi watsi da lamarin ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kailani Muhammad ya bukaci shugaban kasa Tinubu da kada ya damu da ziyarar da tsohon sarkin Kanon ya kai masa, yana mai bayyana su a matsayin dabarun neman jan hankali.

Jigon APC ya nemi Tinubu ya binciki Sanusi

Jaridar The Sun ta nakalto Kailani yana cewa:

"Muna ta ganin tsohon gwamnan CBN, Sanusi Lamido, kusa da fadar shugaban kasa da sauran wuraren gwamnati kuma wannan ne tushen damuwarmu. Muna so mu ba da shawarar cewa kada shugaban kasa ya saurare shi.
"A zahirin gaskiya, muna so a fadada bincike zuwa zamaninsa a matsayin tsohon gwamnan CBN. Akwai batutuwa da dama a wuyansa wanda ya sa tsohon shugaban kasa Jonathan ya dakatar da shi.

Kara karanta wannan

"Kada Ka Sake Shi": Asari Dokubo Ya Fada Ma Tinubu Hatsarin Da Ke Tattare Da Sakin Nnamdi Kano

"Mun kusa san cewa Emefiele yaronsa ne. Ya kamata shugaban kasa ya bincike shi tare da Emefiele don su fito da kudinmu saboda dalilai na ci gaba."

Girman kan Tinubu zai kai shi ya baro, Inji Charly Boy

A wani labari na daban, mawakin Najeriya Charles Oputa wanda aka fi sani da Charly Boy ya yi martani a kan tsige shugabannin tsaro da nada sabbi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi.

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter, Charly Boy ya nuna rashin jin dadinsa ga yan Najeriya da suke jinjinawa shugaban kasar kan yadda yake tafiyar da harkokin gwamnati a baya-bayan nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel