Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido a Villa

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido a Villa

  • Shugaba Tinubu ya shiga ganawar sirri da Sarkin Kano na 14, Sanusi Lamido Sanusi a fadarsa da ke Abuja ranar Alhamis
  • Wannan dai shi ne karo na farko da Sanusi ya ziyarci shugaba Tinubu tun da aka rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayu, 2023
  • Babu cikakken bayani kan batun da zasu tattauna har kawo yanzu, sai dai zaman ya zo mako ɗaya bayan Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga ganawa yanzu haka da Sarkin Kano na 14 kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Sanusi Lamido Sanusi, a fadarsa da ke Abuja.

Channels tv ta tattaro cewa wannan ziyara da Sanusi ya kai wa shugaban kasa yau Alhamis, 15 ga watan Yuni, ita ce ta farko tun bayan da Tinubu ya hau kan madafun iko.

Kara karanta wannan

Manyan Jiga-Jigai 2 Sun Gana da Shugaba Tinubu a Villa, Sun Yi Bayani Mai Jan Hankali

Sanusi da shugaba Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido a Villa Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Sanusi Lamido Sanusi
Asali: Twitter

Haka nan wannan ganawa na zuwa ne mako guda bayan shugaban ƙasa Tinubu ya dakatar da Mista Godwin Emefeliele daga matsayin gwamnan CBN.

Wane batutuwa zasu tattauna a taron?

Har kawo yanzun ba'a bayyana muhimman batutuwan da shugaban ƙasa Tinubu zai tattauna da Sanusi ba yayin wannan zama a Villa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanusi ya yi aiki a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) daga watan Yuni, 2009 zuwa watan Yuni, 2014 lokacin da Emefiele ya gaje shi.

Yadda Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN

A ranar Jumu'a da ta gabata, shugaban ƙasa ya dakatar da Emefiele daga matsayin gwamnan CBN kuma ya umarci mataimakinsa na sashin ayyuka ya maye guribin.

Washe gari ranar Asabar, hukumar 'yan sandan farin kaya ta ƙasa (DSS) ta tabbatar da cewa tsohon gwamna CBN, Mista Emefiele, yana tsare a hannunta.

Kara karanta wannan

Abubuwa 4 Da Ake Ganin Suna Da Alaka Da Dakatar Da Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa Da Tinubu Ya Yi

Bayan nan a ranar Laraba, babban bankin Najeriya ya fara kokarin daidaita farashin musaya inda ya haɗa dukkan wata kasuwar canjin kuɗi a Najeriya zuwa wuri ɗaya, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Yakasai da Bisi Akande Sun Gana da Shugaba Tinubu a Aso Rock

A wani rahoton na daban Dattawan kasa Bisi Akande da Tanko Yakasai, sun ziyarci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja.

Manyan jiga-jigan sun yaba da kamun ludayin sabon shugaban ƙasan, inda aka ji suna cewa 'yan Najeriya na cikin farin ciki a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel