Yakasai da Bisi Akande Sun Gana da Shugaba Tinubu a Aso Rock

Yakasai da Bisi Akande Sun Gana da Shugaba Tinubu a Aso Rock

  • Alhaji Tanko Yakasai da Bisi Akande sun ziyarci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a fadarsa da ke Abuja ranar Alhamis
  • Bayan gana wa da Tinubu, Dattawan kasan sun bayyana cewa sun gamsu da kamun ludayin wannan gwamnati
  • Tanko Yakasai ya tuna lokacin da Tinubu ya kai masa ziyara har gida gabanin tsayawa takarar kujera lamba ɗaya

Abuja - Dattawan ƙasa, Alhaji Tanko Yakasai da Chief Bisi Akande, sun ziyarci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a fadarsa Aso Rock ranar Alhamis, 15 ga watan Yuni.

Manyan jiga-jigan sun yaba da kamun ludayin sabon shugaban ƙasan, inda aka ji suna cewa 'yan Najeriya na cikin farin ciki a yanzu, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Tanko Yakasai da shugaba Tinubu.
Yakasai da Bisi Akande Sun Gana da Shugaba Tinubu a Aso Rock Hoto: @thecable
Asali: Twitter

Dattawan biyu, waɗanda ake wa kallon abokanan Tinubu a siyasa, sun bayyana haka ne yayin zantawa da yan jaridan gidan gwamnati a Abuja bayan ganawa da Tinubu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Sanya Labule Da Abdulsalam Abubakar a Villa, Bayanai Sun Fito

A hangensu, Yakasai da Akande sun ce shugaban kasa Tinubu zai nuna wa duniya banbancinsa da sauran shugabannin da aka taɓa yi a baya a ƙasar nan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Meyasa dattawan suka ziyarci shugaba Tinubu?

Da yake jawabi, Alhaji Tanko Yakasai, ya tuna lokacin da Tinubu ya kai masa ziyara kuma ya nemi shawarinsa da albarka gabanin ayyana kudirin neman takarar shugaban ƙasa.

A cewarsa, bisa la'akari da haka, yanzu lokaci ne da ya kamata ya ziyarce shi domin taya murna da kuma tabbatar masa da goyon baya, The Cable ta tattaro.

Yakasai ya ƙara da cewa ya gamsu cewa Tinubu zai kawo ci gaba da kafa ayyukan raya ƙasa kamar yadda aka ga ya aiwatar a jihar Legas.

A kalamansa ya ce:

"Mun ƙosa, muna Allah-Allah Ubangiji ya kawo mana wani kamar Asiwaju ya zama shugaban Najeriya. Tun daga Abubakar Tafawa Balewa, bamu sake samun shugaban kasa mai ajin siyasa ba sai Asiwaju."

Kara karanta wannan

Abubuwa 4 Da Ake Ganin Suna Da Alaka Da Dakatar Da Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa Da Tinubu Ya Yi

"Ni ɗan siyasa ne, na haura shekaru 60 ana damawa da ni a siyasa kuma na san cewa 'yan siyasa ne kaɗai zasu gyara kasar nan kamar yadda suka yi a wasu kasashe."

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido a Villa

A wani labarin kuma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga ganawar sirri da tsohon sarkin Kano kuma tsohon gwamnan CBN, Sanusi Lamido Sanusi a Villa.

Wannan ne karo na farko da aka ga Sanusi a fadar shugaban kasa tun da Bola Tinubu ya karɓi akalar shugabancin Najeriya a watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel