Abubuwa 11 da Suka Taimaki Tajudden Abbas Ya Zama Shugaban Majalisar Wakilai
- Tajudden Abbas ya lashe zaben da aka gudanar a yau, ya dare kujerar shugaban majalisar wakilai
- ‘Dan majalisar ya samu 98% na kuri’un da aka kada a zabe, ya doke sauran masu neman takarar
- An tsaida shugaban majalisar ne ta hanyar yin zabe a fili, ‘Yan majalisa 353 su ka goyi bayan Abbas
Abuja - A wannan rahoto, mun yi nazarin wasu manyan dalilan da suka taimakawa Hon. Tajudden Abbas wajen zama sabon shugaban majalisar wakilan kasar.
1. APC ta zabi Abbas/Kalu
Tun farko jam’iyyar APC ta nuna inda ta sa gaba, ta ware kujerun majalisar zuwa kowane yanki, a majalisar wakilai ta tsaida Tajuddeen Abbas da Ben Kalu.
Hakan ya jawo har wasu jiga-jigan ‘yan adawa sun yi biyayya ga matakin da APC mai mulki ta dauka illa wasu daga Arewa maso tsakiya a farkon lamarin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
2. Goyon bayan Bola Tinubu
Sabon shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi zama dabam-dabam da masu takara domin ganin sun janyewa Tajudden Abbas PhD, kuma hakan ya yi tasiri sosai.
Idan za a tuna irin rashin tsoma bakin ne ya ba Bukola Saraki da Yakubu Dogara sa’a a 2015. Wannan karo fadar shugaban kasa ta samu goyon har 'yan adawa.
3. Gwamnonin APC
Baya ga jam’iyya, kusan duka Gwamnoni face irinsu Rotimi Akeredolu sun bi bayan jam’iyya. Wasu gwamnonin PDP sun umarci ‘yan majalisunsu da su yi biyayya.
4. Femi Gbajabiamila
Femi Gbajabiamila ya fito karara ya goyi bayan Abbas ya zama sabon shugaban majalisar wakilai. Watakila hakan ya jawo sabani tsakaninsa da mataimakinsa.
5. Alfarmar Nasir El-Rufai
Jim kadan bayan zaben 2023 aka ji Nasir El-Rufai (a lokacin yana Gwamna), ya na cewa zai roki alfarmar Bola Tinubu domin ‘dan majalisarsa ya yi nasara.
Majalisa Ta 10: Tsohon Minista Ya Ce Kirista Dan Kudu Ya Dace Ya Gaji Kujerar Lawan, Soki Sauran Masu Nema
6. Abbas ya fi karfin G7
An dauki lokaci mai tsawo ba tare da ‘yan kungiyar G7 sun fitar da ‘dan takara a cikinsu ba. Ana haka Alhassan Doguwa ya fice, Mukhtar Betara kuma ya janye.
Baya ga Hon. Betara, janye takarar Hon. Yusuf Gagdi ta ragewa tafiyar karfi. Ragowar ‘yan takarar ba su iya fitar da mutum daya kamar yadda suka yi alkawari ba.
7. Goyon bayan manyan Majalisa
Legit.ng Hausa ta fahimci ‘yan Joint Task Force sun taka rawar gani wajen tallata Iyan Zazzau, haka zalika gogaggun ‘yan majalisa irinsu Alhassan Ado Doguwa.
8. Tarihin Tajuddeen Abbas a Majalisa
Ganin kokarin da Abbas ya yi a majalisa daga 2015 zuwa yau ya taimakawa abokan aikinsa wurin mara masa baya, sannan shi a karon kansa, bai yi fada da kowa ba.
9. An ba Arewa ta tsakiya kujerar SGF
Mutanen Arewa maso tsakiya sun koka kan yadda aka ware su a rabon mukaman majalisa, amma nada George Akume daga yankin a matsayin SGF, ya rufe masu baki.
10. Arewa maso yamma
A majalisa babu yankin da ya kai Arewa maso yamma yawan kujeru (92), ware kujerar ga mutumin Kaduna ya sa ya samu magoya baya daga bangarensa.
11. Yanayin zaben da aka yi
Legit.ng ta ce tsarin zabe da aka fito da shi ya taimaki ‘dan takaran na APC, ‘yan majalisa za su ji tsoron a same su karara su na sabawa umarnin da jam’iyya ta bada.
An zabi Benjamin Kalu
A rahoton da mu ka fitar dazu, an ji Benjamin Kalu daga Abia ya zama mataimakin shugaban majalisar wakilai, ya dare kujerar ne ba tare da adawa ba.
Jimi Benson mai wakiltar Ikorodu a Legas ya tsaida Hon. Kalu, sai Khadijat Abba-Ibrahim daga Yobe ta mara masa baya ya maye gurbin Ahmad Wase.
Asali: Legit.ng