Gwamnonin APC Sun Fadi Waɗanda Suka Fi Cancanta da Shugabancin Majalisar Tarayya

Gwamnonin APC Sun Fadi Waɗanda Suka Fi Cancanta da Shugabancin Majalisar Tarayya

  • Gwamnonin jihohin APC su na tare da shugabannin jam’iyyar a game da zaben majalisar tarayya
  • Sanata Hope Uzodinma ya zauna da ‘yan kungiyar Joint Task force da ke tallata Tajuddeen Abbas
  • Shugaban kungiyar Gwamnonin APC ya ce Tajuddeen Abbas/Ben Kalu sun fi dacewa da shugabanci

Abuja - Shugaban kungiyar PGF ta gwamnonin jam’iyyar APC, Hope Uzodinma ya nuna goyon bayansu ga ‘yan takaran da aka tsaida a zaben majalisa.

Vanguard ta rahoto Hope Uzodinma ya na yabawa zabin Tajuddeen Abbas da Benjamin Kalu a matsayin shugaban majalisar wakilai da mataimakinsa.

Mai girma Gwamnan ya bayyana haka a lokacin da ya karbi ‘yan kungiyar Joint Task a gidan Gwaman jihar Imo da ke unguwar Asokoro a birnin Abuja.

Gwamnonin APC
Gwamnonin APC a Aso Rock Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Sanata Uzodinma ya ce jam’iyyarsa ta APC mai mulki ta zakulo wadanda suka fi cancanta a takarar shugabancin majalisa, ya ce PGF ta na goyon bayansu.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan PDP Ya Taimaki APC Wajen Raba Kan ‘Yan Adawa a Zaben Majalisa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya nuna kungiyarsa za ta yi kokarinta na ganin an rantsar da Abbas da Kalu a ranar 13 ga watan Yunin da za a kaddamar da sabuwar majalisa.

Rahoton ya ce Uzodinma ya yabi ‘yan wannan kungiyar hadaka da ke tallata takarar Abbas/Kalu, ya ce sun canki mai ci da suke goyon bayan ‘yan takarar.

A lallashi sauran 'yan takara

Daga cikin shawarar da Gwamnan na jihar Imo ya bada shi ne ‘yan takaran su lallashi sauran masu harin mukaman, ya ce hakan zai kawo hadin-kai.

A cewar Uzodinma, idan aka hada-kai da bangaren zartarwa, ‘yan majalisar tarayyar za su fi cin moriyar kujerarsu wajen kai ayyukan cigaba a mazabunsu.

Tsohon Sanatan ya ce tsoma baki da jam’iyya tayi a kan sha’anin majalisar ba katsalandan ba ne.

A samu hadin-kai a gwamnati

Kara karanta wannan

An Shirya Tsaf, 'Yan Kwadago Sun Janye Yajin-Aiki Bayan An Yi Kus-Kus a Aso Rock

“Ba maganar karfa-karfa ba ce, zai amfani dukkaninmu ne, kuma wannan hadin-kai zai taimaka mana wajen taimakawa mutanenmu a gida.
Ba za ku so a koma gida bayan shekaru hudu ba, ya zama babu abin da za a iya nunawa na aikin da aka yi wa mutane a dalilin rashin hadin-kai.”

- Hope Uzodinma

Wike zai yi wa PDP illa

A zaben shugabannin majalisa, an ji labari tsohon Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya karkata ga Tajuddeen Abbas da jam’iyyar APC ta tsaida.

Da alama manyan ‘yan jam’iyyar NNPP da wakilan ADC duk sun bi bayan Tajuddeen Abbas/Ben Kalu, watakila zai yi wa ‘yan adawa wahalar kai labari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel