Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Rantsar Da Geoge Akume a Matsayin Sabon SGF

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Rantsar Da Geoge Akume a Matsayin Sabon SGF

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Sanata George Akume a matsayin sabon sakataren gwamnatin tarayya
  • George Akume wanda tsohon gwamnan jihar Benue ne kuma tsohon minista zai kama sabon aikinsa gadan-gadan
  • Manyan ƙusoshi ne dai suka halarci rantsar da Akume da shugaba Tinubu ya yi a matsayin sabon sakataren gwamnatin tarayya

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rantsar da Sanata George Akume, a matsayin sabon sakataren gwamnatin tarayya (SGF), a zauren majalisar zartarswa ta ƙasa da ke a fadar shugaban ƙasa.

Jaridar Channels Tv ta kawo rahoto cewa Sanata George Akume, ya yi rantsuwar kama aiki ne, a bikin wanda ya samu halartar manyan jiga-jiga da suka haɗa da wasu gwamnoni da tsaffin gwamnoni.

Tinubu ya rantsar da sabon SGF
Shugaba Tinubu da George Akume Hoto: @Channelstv
Asali: Twitter

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya FolasadeYemi-Esan da matar sabon SGF ɗin, Mrs Regina Akume, sun halarci rantsuwar.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sanya Labule Da Masu Neman Shugabancin Majalisa, Bayanai Sun Fito

Shugaba Tinubu ya yi naɗe-naɗen farko

Wannan bikin dai na zuwa ne kusan kwanaki biyar bayan shugaban ƙasar ya sanar da naɗin kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin tarayya, cewar rahoton Punch

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wannan ranar ne kuma shugaba Tinubu ya sanar da naɗin Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, tsohon gwamnan jihar Jihawa, a matsayin mataimakin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin tarayya.

A taron da shugaban ƙasar ya yi da gwamnonin jam'iyyar APC, ya kuma sanar da naɗin tsohon gwamnan jihar Benue kuma tsohon ministan ayyuka na musamman a matsayin sakataren gwamnatin tarayya (SGF).

Sanarwar ta kuma bayyana cewa sabon sakataren gwamnatin tarayyar zai kama aikinsa nan ta ke ba tare da ɓata lokaci ba.

Majalisa Ta Amince Tinubu Ya Yi Manyan Nade-Nade 20

A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa majalisar dattawa ta amince da wata buƙata da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar gabanta domin yin nazari.

Kara karanta wannan

"First Lady": Matar Shugaban Kasa, Oluremi Tinubu, Ta Shiga Ofis, Ta Fara Aiki Gadan-Gadan

Majalisar dattawan ta amince da buƙatar sabon shugaban ƙasar na ya naɗa masu ba shi shawara na musamman har mutum 20. Shugaban ƙasar bai bayyana ko su wanene mutum 20 ɗin da zai ba waɗannan muƙaman ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel