El-Rufai Ya Fadi Alfarma 1 Da Yake Nema Wajen Tinubu Saboda Gudumuwar da Ya Bada

El-Rufai Ya Fadi Alfarma 1 Da Yake Nema Wajen Tinubu Saboda Gudumuwar da Ya Bada

  • Nasir Ahmad El-Rufai yana goyon bayan shugabancin majalisa ya fada hannun Abbas Tajudeen
  • Hon. Abbas Tajudeen ya yi nasarar komawa majalisar wakilan tarayya a karkashin APC
  • Gwamnan zai dage wajen ganin ‘Dan majalisar na yankin Zariya ya samu mukami na hudu a kasa

Kaduna - Nasir Ahmad El-Rufai ya yi kira ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da ya goyi bayan Hon. Abbas Tajudeen ya zama shugaban majalisar wakilai.

The Nation ta ce Mai girma Nasir Ahmad El-Rufai yana goyon bayan ‘dan majalisar na Zariya ya gaji Rt. Hon. Femi Gbajabiamila a majalisar tarayya.

A ranar Lahadin nan, Gwamnan jihar Kaduna ya zanta da magoya bayan jam’iyyar APC a garin Zariya, ya nuna masu burinsa game da Hon. Tajuddeen.

Gwamna Nasir El-Rufai ya ji dadi da ganin yadda tsohon ‘dan majalisar ya sake lashe zabensa a 2023.

Kara karanta wannan

Gwamnan CBN Ya Shiryawa Tinubu Sababbin Makarkashiya a Zaben Gwamnoni

Mutane su na goyon bayan Iyan Zazzau

Iyan na Zazzau ya doke ‘dan takaran jam’iyyar PDP, Shuaibu Musa Indabo da Hpn. Sulaiman Ibrahim Dabo na jam’iyyar LP wajen samun tazarce na uku.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An rahoto Nasir El-Rufai yana mai cewa dinbin mutane su na ta aiko sako cewa a goyi bayan ‘dan majalisar na Zariya ya zama sabon shugaban majalisa.

Tinubu El-Rufai
Gwamna El-Rufai da Bola Tinubu Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Gwamnan ya nuna yana bibiyar abin da mutane suke nema, kuma ya nuna zai nemi alfarma wajen zababben shugaban kasa domin ganin hakar ta cin ma ruwa.

El-Rufai ya yi niyyar zuwa har Legas domin ya hadu da shugaban kasar mai jiran gado a game da maganar kujerar shugaban majalisa da Kaduna ta ke nema.

Malam El-Rufai ya ce ya fasa zuwa Legas din domin Tinubu zai zo birnin Abuja a karshen makon jiya, a nan ake sa ran Gwamnan na Kaduna zai gana da shi.

Kara karanta wannan

Bago VS Kantigi: Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Manyan Yan Takara 2 a Jihar Neja

Yanzu haka Hon. Abbas Tajudeen shi ne shugaban kwamitin sufuri na kasa a majalisar tarayya, tun 2011 yake wakiltar mutanen Birnin Zariya da kewaye.

"Amma babban abin da zan nema ni dai idan na bada gudumuwa a wannan zaben da wannan tafiya ta Asiwaju, yadda za a biya ni kawai, shi ne Iyan Zazzau ya zama shugaban majalisa."

- Nasir El-Rufai

Rigingimun cikin gida a 2023

Ku na da labari cewa har yanzu akwai kura a jihohin Benuwai, Ogun, Bauchi, Abia, Enugu, Oyo, Ribas, Edo, Katsina, Ekiti, Delta da Kwara a zaben Gwamnoni.

Alal misali Rt. Hon. Yakubu Dogara yana goyon bayan ‘dan takaran APC a Bauchi, Uzor Kalu yana marawa kaninsa baya ne a APP a zaben Gwamnan Abia.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel