Shugaban Majalisar Dattawa: Gwamnoni Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Zabin Tinubu

Shugaban Majalisar Dattawa: Gwamnoni Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Zabin Tinubu

  • Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana dan takarar da ya fi so don zama shugaban majalisar dattawa na gaba yayin da ake shirin rantsar da majalisa ta 10
  • Makinde ya ce shi da takwarorinsa za su kasance a majalisar dokokin tarayya don shaida tsarin zaben shugabannin
  • A cewar gwamnan, shi da takwarorinsa suna tare da dan takarar da shugaban kasa Bola Tinubu ke so don darewa wannan kujera

Oyo - Gwamnan jihar Oyo kuma jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Seyi Makinde, ya bayyana cewa wanda shugaban kasa Bola Tinubu ke so ya zama shugaban majalisar dattawa na gaba shine wanda takwarorinsa ke so ya jagoranci majalisar tarayya ta 10.

Makinde ya fadi haka ne yayin da yake jawabi a ranar Litinin, 12 ga watan Yuni, lokacin bikin godiya na bayan rantsar da shi a karo na biyu a Ibadan, babban birnin jihar gabannin rantsar da majalisar tarayyar wanda za a yi a ranar Talata, 13 ga watan Yuni, rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa da Tinubu, Gwamnan APC Ya Faɗi Sanatan da Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa

Logon PDP da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo
Shugaban Majalisar Dattawa: Gwamnoni Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Zabin Tinubu Hoto: Seyi Makinde
Asali: Twitter

Gwamnoni sun hadu don marawa dan takarar Tinubu baya wajen zama shugaban majalisar dattawa, Makinde ya bayyana

Gwamnan ya yi jawabi a wajen taron wanda kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) reshen jihar Oyo ta shirya don karrama shi, rahoton Punch.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Makinde ya bayyana cewa gwamnonin sun hadu don marawa zabin Tinubu na shugaban majalisar dattawa kirista daga yankin kudu maso kudancin kasar baya.

Makinde ya sha alwashin kasance a majalisa don kula da zaben shugaban majalisar dattawa

Wani bangare na jawabinsa ya ce:

"Ba ma siyasar addini amma abun da yake daidai shine daidai. Mun tsaya tsayin daka don samun shugaban kasa dan kudu; mun tsaya ga gaskiya, adalci kuma za mu tsaya kan daidaito shima."

Gwamnan ya kuma sha alwashin kasancewa a majalisar dokokin tarayya tare da takwarorinsa a ranar Talata sannan za su tabbatar da ganin cewa an yi gaskiya, daidai da adalci a zaben shugaban majalisar dattawa.

Kara karanta wannan

Hotuna Da Bayanai Sun Bayyana Yayin da Tinubu Ya Karbi Bakuncin Akpabio Da Hope Uzodimma a Villa

An shirya za a gudanar da zaben shugabancin majalisa ta 10 a ranar Talata, 13 ga watan Yuni.

Ka halarci zaman kotun zabe don marawa Atiku baya: Melaye ga Makinde

Legit.ng ta rahoto a baya cewa dan takarar gwamnan PDP a zaben jihar Kogi mai zuwa, Dino Melaye, ya baiwa Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo sharadi guda da zai tabbatar da yunkurinsa na yin sulhu da Atiku Abubakar.

Da yake martani ga ikirarin Makinde na cewar PDP ta fara farfadowa, Melaye ya bukaci gwamnan ya halarci zaman kotun zaben shugaban kasa na 2023 don nuna goyon baya ga Atiku da PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel