2023: Ana Zaman Lafiya, Alkali Ya Ce Ministan Buhari Ya Biya Miliyoyi ga Atiku Abubakar

2023: Ana Zaman Lafiya, Alkali Ya Ce Ministan Buhari Ya Biya Miliyoyi ga Atiku Abubakar

  • Festus Keyamo SAN bai yi nasara a karar da ya shigar a kotun tarayya a kan Alhaji Atiku Abubakar ba
  • James Omotosho ya yanke hukunci cewa tsohon Ministan zai biya kudi ga ‘dan takaran da kuma ICPC
  • Lauyoyin Keyamo ba su gamsu da hukuncin da aka yi a kotun na Abuja ba, za su tafi kotun daukaka kara

Abuja - Babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja tayi umarni ga Festus Keyamo SAN ya biya tarar Naira miliyan 10 a shari’arsa da Atiku Abubakar.

Daily Trust ta kawo rahoto cewa a hukuncin da ya zartar, Mai shari’a James Omotosho ya bukaci Festus Keyamo ya ba dan takaran Naira miliyan 5.

Haka zalika tsohon Ministan kwadago da samar da ayyukan yi zai biya ICPC Naira miliyan 5.

Kara karanta wannan

Binciken Majalisa Ya Tsumbula Gwamnatin Buhari a Badakalar Naira Biliyan 910

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar a masallacin Juma'a Hoto: @Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Omotosho wanda ya saurari shari’ar ya yi kaca-kaca da mai karar, yake cewa an nemi ayi wasa da kotu don haka ya zartar da wannan hukunci.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Za a biya kudin sannun a hankali

Rahoton ya ce Alkalin ya bada umarni a rika biyan 10% na kudin a duk shekara har a kammala biya, hakan ya na nufin za a dauki shekara da shekaru.

Keyamo ya shigar da wannan kara mai lamba FHC/ABJ/CS/84/2023 ne a watan Junairu, ya na neman kotu ta tilastawa EFCC da CCB binciken Atiku.

Lauyan Atiku Abubakar watau Benson Igbanoi da kuma Oluwakemi Odogun wanda ya tsayawa hukumar ICPC duk sun bukaci ayi fatali da shari’ar.

Maganganun Michael Achimugu

Tsohon kakakin kwamitin na yakin neman zaben Tinubu-Shettima ya fake ne da wasu kalamai da ake zargin sun fito daga bakin Mista Michael Achimugu.

Kara karanta wannan

“Sai An Tauna Tsakuwa Idan Za a Kai Najeriya Gaba”: Wike Ya Goyi Bayan Tinubu Kan Cire Tallafin Mai

Ana zargin an ji Achimugu wanda ya yi aiki da tsohon mataimakin shugaban kasar ya na bayanin yadda aka rika satar dukiyar al’umma a lokacin mulkinsu.

A dalilin haka ne Keyamo ya zargi ‘dan takaran na PDP da saba dokokin kasa, ya dauki hayar lauya ya je kotu domin ganin hukumomi sun bincike shi.

Ba ayi nasara a kotu ba

Punch ta ce John Ainetor (Esq) ya fitar da jawabi ya na cewa za su daukaka kara domin Keyamo bai gamsu da hukuncin da kotun tarayyar ta yanke ba.

Ainetor ya ce sun je kotu ne domin hukumomin yaki da rashin gaskiya su binciki tsohon mataimakin shugaban kasar, yanzu za a tafi kotun daukaka kara.

Binciken 'Yan majalisa

Majalisar dattawa ta bankado batun kudin da ake cewa hukumomin gwamnati sun karbi aro. Kwamitin Sanata Matthew Urhoghide ne ya gano wannan.

Sanatoci sun fahimci bayan shekara da shekaru, kudin da aka karbi bashi ba su dawo ba, an samu labari an yi wannan ne da yardar Akanta Janar na kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel