Cire Tallafin Man Fetur: Reno Omokri Ya Lissafa Muhimman Sharudda 4 Da Ya Kamata Gwamnatin Tinubu Ta Cika

Cire Tallafin Man Fetur: Reno Omokri Ya Lissafa Muhimman Sharudda 4 Da Ya Kamata Gwamnatin Tinubu Ta Cika

  • Reno Omokri, tsohon babban mataimaki na musamman ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a shafukan sada zumunta, ya ce yana goyon bayan cire tallafin man fetur da aka yi
  • Omokri ya yi nuni da cewa dama cire tallafin man fetur na daga cikin manufofin jam’iyyarsa ta PDP
  • Tsohon hadimin tsohon shugaban ƙasar ya zayyano wasu sharuddan da ya ce dole ne shugaba Bola Tinubu ya cika domin samun goyon bayan ‘yan Najeriya

FCT, Abuja - Tsohon hadimin shugaban ƙasa Jonathan, Reno Omokri, a ranar Laraba, 31 ga watan Mayu, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga cire tallafin man fetur da gwamnatin Bola Tinubu ta yi.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Omokri ya bayyana cewa jam’iyyarsa ta PDP ma irin ƙudirinta kenan, haka nan ma 'yan takararta.

Reno Omokri ya goyi bayan Tinubu kan batun cire tallafi
Reno Omokri, ya ce ya goyi bayan cire tallafin man fetur da Tinubu ya yi. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Reno Omokri
Asali: Facebook

Reno ya bayar da sharuddan da ya kamata gwamnati ta cika

Reno Omokri ya bayyana cewa yana goyon bayan cire tallafin man fetur ɗin da Tinubu ya yi, amma kuma ya zayyanu wasu sharuɗa guda huɗu da yake ganin ya kamata gwamnati ta cika su, sharuɗɗan sune:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. Albashi

Reno Omokri ya ce dole ne gwamnati ta yi koƙarin ƙara albashin ma’aikata.

2. Matsalar canjin kuɗi

Reno ya ce dole ne babban bankin Najeriya (CBN ) ya yi ƙoƙari wajen daidaita farashin kuɗaɗen Najeriya a wajen canjinsu da kudaden waje.

3. Bayar da tallafi ga marasa karfi

Dole ne gwamnati ta bayar da tallafi ga kaso 5% na 'yan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi.

4. Batun kudaden tsofaffin shugabanni

A dakatar da batun bayar da N63bn da ake son bai wa Buhari, Osinbajo da gwamnonin da suka sauka daga kujerunsu har sai an aiwatar da abubuwa ukun da ke sama.

Reno ya ce idan aka cika waɗannan sharuɗa da ya zayyano, to yana da kyau duk wani ɗan ƙasa na gari ya goyi bayan shirin yi wa ɓangaren man garambawul.

Cire tallafin man fetur ya jefa 'yan Najeriya cikin kunci

Direbobin motocin haya a ranakun Talata, 30 ga watan Mayu da Laraba, 31 ga watan Mayu, sun ƙara kuɗaɗen hawa mota a garuruwa daban-daban na Najeriya.

Hakan ya biyo bayan irin dogon layin da ake samu a gidajen mai, sakamakon cire tallafin man fetur da aka yi.

A mafi yawa daga cikin wurare, farashin sufurin ya ƙaru da sama da 100% kan yadda ake biya a baya.

Bangare na gaba da ya kamata Tinubu ya duba bayan cire tallafin mai

A wani labarin na daban, ana ganin cewa ba iya batun tallafin man fetur ba ne kaɗai ya kamata Tinubu ya yaƙa a gwamnatinsa, akwai maganar kasuwar 'yan canjin kuɗi ta ƙasa.

Mutane da dama na ganin cewa kasuwar canjin kuɗaɗe ta bayan fage na taka muhimmiyar rawa wajen ƙara lalata darajar da kuɗin Najeriya wato Naira ke da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel