Tsohon Gwamnan Ribas, Wike Ya Jima da Barin Jam'iyyar PDP, In ji Mamban NEC

Tsohon Gwamnan Ribas, Wike Ya Jima da Barin Jam'iyyar PDP, In ji Mamban NEC

  • Mamban NEC-PDP na ƙasa, Timothy Osadolor, ya nuna cewa tuni jam'iyyar PDP ta raɓa gari da tsohon gwamnan Ribas
  • Ya ce Nyesom Wike ya jima da rasa martabarsa a inuwar PDP kuma shi kansa idan zai faɗi gaskiya ya san ba ɗan jam'iyya bane
  • Sai dai tsohon kwamishinan yaɗa labarai da sadarwa a gwamnatin Wike ya maida martani kan waɗannan kalamai

Mamban kwamitin ƙoli na jam'iyyar PDP ta ƙasa (NEC), Timothy Osadolor, ya ce tsohon gwamnan jihar Ribas da ya sauka, Nyesom Wike, ba mamban PDP bane yanzu.

Jigon babbar jam'iyyar hamayya ta ƙasa ya nuna cewa bisa la'akari da abinda Wike ya aikata gabanni, lokacin da kuma bayan babban zaben 2023, an daina masa kallon ɗan PDP.

Gwamna Wike.
Tsohon Gwamnan Ribas, Wike Ya Jima da Barin Jam'iyyar PDP, Inji Mamban NEC Hoto: Nyesom Wike
Asali: UGC

Mista Osadolor ya yi wannan bayani ne yayin tattaunawa da jaridar Punch ta wayar salula ranar Talata, 30 ga watan Mayu, 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Babban Jigon PDP Kuma Shugaban AIT Ya Mutu Ranar da Tinubu Ya Hau Gadon Mulki

Ya bayyana cewa shugabannin jam'iyya na ƙasa sun ɗauki matakin killace Wike da kuma maida shi gefe a harkokin tafiyar da jam'iyyar PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa, Osadolor ya ce:

"Jam'iyyar PDP ta jingine Wike saboda shi kansa bai san meke masa ciwo ba, akwai hanyoyin magance mutane da dama ba tare da an hukunta su ba. Zaka iya killace mutum wuri ɗaya ya zama mara amfani."
"Zai iya cewa ai shi ne ya tsame hannu daga al'amuran PDP amma ai zai fi masa kyau ya ja baya tunda ko ya zo babu wanda zai kula shi. A kaikaice mu ke hukunta shi saboda yana tutiya Kotu ta hana a dakatar da shi."
"Amma ai babu Kotun da ta umarci kar a jingine shi gefe guda. Wannan ne matakin da PDP ta ɗauka, idan Wike zai faɗa muku gaskiya, zai ce shi ba mamban PDP bane domin babu ɗan PDPn da zai yi abinda ya aikata."

Kara karanta wannan

Rantsar Da Tinubu: Datti Baba-Ahmed Ya Dau Zafi, Ya Aike Da Muhimmin Sako Ga 'Yan Najeriya

Wannan ba gaskiya bane Inji Tsohon kwamishinan Wike

Da yake maida martani, jigon PDP a jihar Ribas kuma tsohon kwamishinan yaɗa labarai da sadarwa, Chris Finebone, ya ce har yau Wike cikakken mamban PDP ne.

Yayin da yake ayyana kalaman Osadolor a matsayin shafcin gizo, Finebone ya ce ba shi da ikon magana a madadin jam'iyyar PDP.

"Bamu san da yawun wa yake wannan kalaman ba, amma duk tunaninsa ne kawai. Duk kalaman da ya faɗa ba su da amfani, kuma mai girma tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike mamban PDP ne 110%."

Gwamna Kwara Ga Yan Kasuwa: Duk Wanda Ya Boye Fetur Zan Kwace Lasisinsa

A wani rahoton na daban Gwamnan Kwara ya gargaɗi 'yan kasuwar man Fetur, ya ce zai soke masu lasisi idan suka boye fetur.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Gwamna AbdulRazak ya ce duk gidan man da aka kama yana ɓoye man Fetur, zai soke lasisin hakkin mallakarsa.

Kara karanta wannan

"Bana Tsoron EFCC" Gwamnan Arewa Ya Cika Baki, Ya Ce Ba Inda Zai Je Bayan Miƙa Mulki

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel